in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Iraqi sun yi faretin ayyana nasarar kwace iko da yankunan kasar daga IS
2017-12-11 10:06:33 cri

Dakarun Iraqi sun yi fareti a birnin Baghdad, domin murnar kwace iko da dukkan yankunan kasar daga hannun kungiyar IS.

Faretin da aka gudanar da safiyar jiya a dandalin bukukuwa dake yankin da ya kasance mazaunin manyan ofisoshin gwamnati da na jakadancin kasashen waje, ya samu halartar firaministan kasar kuma shugaban rundunonin tsaron kasar Haider al-Abadi.

Bikin ya kuma samu halartar manyan jami'ai daga ma'aikatar tsaro da na harkokin cikin gida.

Jiragen saman yakin da na saukar ungulu sun yi ta shawagi a dandalin, yayin da motocin yaki da na igwa da sauran dakaru suka yi fareti.

A ranar Asabar da dadddare ne Haider al-Abadi ya ayyana nasarar kwace iko da dukkan yankunan kasar da jami'an tsaro suka yi daga hannun kungiyar IS mai kaifin kishin addinni

Sai dai duk da ayyana nasarar da ya yi, firaministan ya gargadi dakarun da su zauna cikin shirin fito na fito da duk wani nau'i na harin ta'addanci da za a iya kai wa al'ummar kasar.

Har wa yau, masu sanya ido sun yi gargadin cewa, sanarwar ta firaministan, ba ta nufin kungiyar ba ta da damar kai hare-hare, domin ta na iya kai hari ta hanyar amfani da mambobinta na sirri dake cikin al'umma. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China