in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin: kasar za ta nemi ci gaba ta fuskar diplomasiyya
2017-12-09 17:21:38 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci wani taron tattaunawa game da yanayin duniya da harkar diplomasiyya ta kasar Sin a shekarar 2017, taron da cibiyar nazarin batutuwan kasa da kasa ta kasar Sin, da asusun nazarin hakokin kasa da kasa na kasar Sin suka shirya a yau Asabar.

A wajen taron, ministan ya bayyana cewa, za a yi kokarin daukar wasu sabbin manufofi, da kara sauke wasu nauyin dake wuyan kasar Sin, bisa kokarin raya harkar diplomasiyya ta kasar a shekarar 2018 mai zuwa, karkashin jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jingping, da kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake kan ragamar mulki.

A cewar jami'in, cikin shekarar 2018, kasar Sin za ta kara kulla huldar abota tare da sauran kasashe, da kokarin gina sabuwar hulda mai inganci tsakanin kasashen duniya. Za ta kuma kara hadin gwiwa da kasashe makwabtan ta, da sauran kasashe masu tasowa, don tabbatar wa al'ummun duniya da wata kyakkyawar makoma ta bai daya. Sa'an nan kasar za ta kara kokarin raya shawarar Ziri daya da Hanya daya, don kasashe daban daban su ci gajiya daga hakan, da kuma lakulo bakin zaren warware wasu batutuwan kasa da kasa masu janyo hankalin jama'ar duniya, tare da kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China