in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta yi wa tsarin mallakar filayen kasar gyaran fuska domin kara janyo jarin waje
2017-12-08 11:31:08 cri

Jiya Alhamis ministan kudin kasar Zimbabwe Patrick Chinamasa ya gabatar da rahoton kasafin kudin gwamnatin kasar na shekarar 2018, inda ya bayyana cewa, kasar za ta yi wa tsarin mallakar filayen kasar gyaran fuska domin kara janyo masu sha'awar zuba jari daga ketare zuwa cikin kasar, wato za a sayar wa 'yan kasashen waje hannun jari, amma ban da fannin hako ma'adinan lu'u lu'u da kuma Platinum.

A yammacin jiya ne, ministan kudin kasar Zimbabwe Patrick Chinamasa ya gabatar wa majalisar dokokin kasar bayanin kasafin kudin kasar na shekarar 2018 mai taken "bullo da sabon tsarin farfado da tattalin arziki", inda ya bayyana cewa, za a yi gyaran fuska ga tsarin mallakar filayen kasar da tattalin arziki domin soke wasu tarnakin da aka sakawa 'yan kasashen waje a fannin sayen hannun jari, ya ce, "Za a ci gaba da aiwatar da dokar sayen hannun jari a fannin sana'ar hakar ma'adinan lu'u lu'u da Platinum, wato dole ne bakaken fata mazaunan kasar su mallaki hannun jarin sama da kaso 51 bisa dari, game da sauran sana'o'in hakar ma'adinai kuwa, ba za a hana kowa sayen hannun jarin ba."

A shekarar 2007 ne, kasar Zimbabwe ta fitar da tsarin mallakar filayen kasar da tattalin arziki, inda aka tanadi cewa, dukkan kamfanonin kasar dake da jarin waje ko karkashin mallakar fararen fata 'yan asalin kasar Zimbabwe wadanda kadarorinsu ya kai sama da dalar Amurka dubu 500, dole ne su sayar da hannun jarinsu kaso 51 bisa dari ga bakaken fata mazauna wurin da aka kafa wadannan kamfanonin, sai dai an fuskanci matsala yayin da ake aiwatar da wannan tsarin, saboda tsarin ya rage sha'awar da 'yan kasuwan kasashen waje ke da ita dangane da wurin da za su zuba jarin su.

A watan Aflilun bara, shugaban kasar na wancan lokaci Robert Mugabe ya bayar da wata sanarwa kan wannan tsarin, inda ya bayyana cewa, an tsara wannan tsari ne a fannin sana'o'in da suka shafi albarkatun halittun kasar ne kawai, yanzu haka an kara bayyana cewa, za a takaita adadin hannun jari da za a zuba a fannin hako ma'adinan lu'u lu'u da Paltinum kawai.

A wannan rana ministan kudin kasar Chinamasa ya bayyana cewa, za a gabatar da shawarar gyaran fuskar tare da dokar kashe kudi ta shekarar 2018 ta kasar ga majalisar dokokin kasar domin neman amincewarta, ana sa ran sabon tsarin zai fara aiki daga watan Aflilun shekara mai zuwa.

Kana game da sana'ar hako ma'adinan lu'u lu'u da Platinum a kasar, idan 'yan kasuwan kasashen waje suka samu izni daga wajen gwamnatin kasar, su ma za su iya mallakar sama da kaso 50 bisa 100 na hannun jarin kamfanin, Chinamasa ya yi bayani cewa, "Idan 'yan kasuwa wadanda ba 'yan asalin kasar Zimbabwe ba sun samu izni daga gwamnatin kasar, misali suna iya samar da guraben aikin yi da dama ga mazauna wurin, ko su koya wa al'umma fasahohi, ko kuma su taka rawa wajen tabbatar da dauwanammen ci gaban kasar, to, ban da sana'ar tace sinadarai, idan suka yi rajista bisa doka a kasar, suna iya ci gaba da tafiyar da harkokin kamfanoninsu a kasar yadda ya kamata."

Ban da haka kuma, Chinamasa ya bayyana a cikin rahotonsa cewa, ya kamata a rage rashin tabbas game da manufofin da gwamnatin kasar ke aiwatarwa, tare kuma da rage kudaden da 'yan kasawa suke bukata wajen tafiyar da harkokin kamfanoninsu a kasar, a sa'i daya kuma, Chinamasa ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi a kara kokari matuka domin yaki da cin hanci da rashawa a kasar, ta yadda za a kara jawo hankalin masu sha'awar zuba jari daga sassa daban-daban na fadin duniya.

Mutane da dama a a bangaren kasuwanci na kasar Zimbabwe sun goyi bayan wadannan matakan da za a dauka, kuma suna ganin cewa, bayanin kasafin kudin zai kyautata yanayin kasuwancin kasar ta Zimbabwe, tare kuma da sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki.

Jagoran kungiyar 'yan kasuwan kasar Zimbabwe Matunda Mugaga ya bayyana cewa, yana cike da imani ga makomar kasarsa, ya ce, "Wannan rahoton,ya mai da hankali kan sake gina kasuwannin kasar da yaki da cin hanci da rashawa, tare kuma da kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasar Zimbabwe da sauran kasashen duniya, duk kan wadannan matakai za su taimaka wajen sake farfado da tattalin arzikin kasarmu, kuma sabbin manufofin da za a dauka da sabbin shirye-shiryen da za a aiwatar sun nuna mana cewa, ko shakka babu tattalin arzikin Zimbabwe zai bunkasa kamar yadda ake fata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China