in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararre: Shawarar ziri daya da hanya daya za ta taimakawa ci gaban tattalin azrikin kasashen Afirka
2017-12-08 10:36:08 cri

Mataimakin shugaban kungiyar dake rajin kare muhalli a majalisar 'yan kasuwar kungiyar tarayyar Turai dake kasar Sin, Gianluca Ghiara ya bayyana cewa, muddin kasashen nahiyar Afirka suka bunkasa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasar Sin karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, babu shakka za su ji ci gajiyar tattalin arziki, da jin dadin rayuwar jama'a da ma muhallin halittu.

Bugu da kari, jami'in ya bayyana cewa, hadin gwiwar kasashen na Afirka da kasar Sin karkashin wannan shawara za ta taimakawa kasashen nahiyar amfana da sabbin fannonin bunkasuwa da ba sa gurbata muhalli.

Ghiara ya ce, hukumomin kasa da kasa sun dora muhimmanci sosai kan shawarar ziri daya da hanya daya, tare da yakinin cewa, shawarar za ta taimakawa ajandar raya nahiyar ba tare da gurbata muhalli ba.

Kasar Sin dai ta samar da kudaden gudanar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa, kamar hanyoyin mota, tashoshin jiragen ruwa da na sama, a wani mataki na saukaka zirga-zirga da abokan huldar ta na ketare karkashin wannan shawara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China