in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ba da lambar yabon kiyaye muhalli ga masu kula da gandun daji na Saihanba
2017-12-06 14:28:56 cri

A jiya Talata ne, a yayin babban taron MDD kan kiyaye muhallin duniya da ya gudana a birnin Nairobin Kenya, MDD ta ba da lambar yabon kiyaye muhalli ga wasu kungiyoyi da mutane guda shida, ciki har da shugabar kasar Chile Michelle Bachelet, da masanin kimiyya na hukumar NASA ta kasar Amurka, Paul A. Newman da mai shirya fina-finai na kasar Amurka, Jeff Orlowski, da babbar darektar kamfanin kekunan haya na Mobike na kasar Sin, Hu Weiwei, da shugaban kamfanin Elion na kasar Sin, Wang Wenbiao, da kuma masu kula da gandun daji na Saihanba na kasar Sin.

Gandun daji na Saihanba yana da tazarar da ba ta kai kilomita 200 ba daga birnin Beijing, babban birnin kasar Sin. A cikin sama da rabin karnin da ya wuce, masu kula da wannan gandun daji sun yi kokarin maido da wannan filin mai rairayi ne zuwa filin bishiyoyi.Zhang Baozhu, wani ma'aikacin gandun daji na Saihanba ya ce, "A baya ana fama da iska da rairayi a wannan yanki. A lokacin bazara, iska tana bugowa hade da dusar kankara, a lokacin kaka kuma, iska na tashi ne tare da rairayi."

A kokarin ganin an gyara wannan mummunan yanayin da ake ciki a yankin, a shekarar 1962, gwamnatin kasar Sin ta kafa gandun daji a yankin na Saihanba.

Madam Chen Yanxian, mai shekaru 73 a duniya, yayin wani jawabi da ta gabatar a madadin dukkanin masu kula da gandun daji na Saihanba a wajen bikin mika lambar yabon, ta tuna da cewa, "Yau shekaru 55 da suka gabata ke nan, a lokacin mu 369 ne muka isa yankin Saihanba, inda ake fama da iska da rairayi, kuma da wuya a gano ciyayi da tsire-tsire. Matsakaicin shekarunmu bai kai 24 da haihuwa ba, kuma a cikin shekaru sama da 50 da suka biyo baya, aiki daya kadai muka gudanar cikin zuriyoyi uku, wato dasa bishiyoyi."

Yankin Saihanba yana kan tudu ne, inda a kan shafe watanni bakwai cikin shekara ana fama da dusar kankara, kuma sanyin wurin zai iya kaiwa kasa da digiri 43 a lokacin dari. Amma duk da mawuyacin hali na rayuwa da mazauna wurin ke fuskanta, abin da ya fi damun masu kula da gandun dajin shi ne yadda kaso 8% na bishiyoyin da aka dasa ne suka rayu cikin farkon shekaru biyu da kafa gandun dajin. Cheng Shun, shugaban sashen kula da bishiyoyi na gandun dajin ya ce, "A farkon lokacin kafa gandun dajin, ana shigowa da tsiron bishiyoyi ne daga waje, mu ba mu iya renon tsiron ba amma shigo da su daga waje ma akwai wahala."

Duk da haka, masu kula da gandun dajin sun yi kokarin daidaita matsalolin da suka fuskanta ta hanyar nazarin kimiyya da kirkire-kirkire da suka yi, har ma suka gano wata hanyar kimiyya ta raya dazuzuka. Sakamakon wannan namijin kokarin, yanzu fadin gandun dajin na Saihanba ya kai eka dubu 74.7, wanda ake daukarsa a matsayin gandun daij mafi fadi a duniya da 'dan Adam ya dasa itatuwa, wanda har ya kare kwararowar hamada daga kudu, har ma ya zama babbar kariya ga manyan biranen Beijing da Tianjin da ke arewacin kasar Sin. Yana kuma jawo masu yawon shakatawa sabo da ni'imarsa. "Yanayin muhalli da iska a yankin yana da kyau sosai, ga yadda sararin samaniya ya kasance mai launin shudi, gaskiya akwai ni'ima."

A yayin bikin ba da lambar yabon, mataimakin babban sakataren MDD, kana shugaban hukumar zartaswa na hukumar kiyaye muhalli ta MDD(UNEP), Erik Solheim ya yaba da nasarorin da masu kula da gandun daji na Saihanba suka cimma, ya ce, "Akwai bukatar farfado da bishiyoyi a duniyarmu. Gandun daji na Saihanba ya shaida mana cewa, bisa ga kokarin da masu kula da gandun daji suka yi cikin zuriyoyi uku, an farfado da dazuzuka masu fadi, wannan ba karamar nasara ba, wadda kuma za ta karfafa wa sauran sassan duniya gwiwa."

Marcelo Furtado, masanin ilmin kiyaye muhalli na kasar Brazil da ya halarci taron kiyaye muhalli na MDD ya ce, masu kula da gandun daji na Saihanba sun cancanci a yi koyi da su, ya ce, "Bisa la'akari da fadin gandun dajin da kuma ilmin da kuka karo da su a yayin raya gandun, musamman ma yadda mutane da dama suka shiga cikin wannan aiki, ina ganin wannan abin ban sha'awa ne, haka kuma tsari ne da ya kamata sauran kasashen duniya ma su koya. Sabo da a kokarin da ake yi na farfado da dazuzuka, ba dasa bishiyoyi ne aiki mafi wahala ba, a'a, aiki mafi wahala shi ne yadda za a rika kula da su, kuma a ganina, wannan na daga nasarorin da mutanen Saihanba suka cimma."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China