in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron Internet na birnin Wuzhen
2017-12-05 18:47:32 cri

A yau Talata ne aka kammala taron kasa da kasa na masu ruwa da tsaki game da yanar gizo ko Internet, karo na 4 a birnin Wuzhen dake gabashin kasar Sin.

Yayin taron na yini 3, an baje kolin sabbin fasahohi, da sassan ci gaba a fannin amfani da Internet. Wakilai daga gwamnatoci, da jagororin hukumomin kasa da kasa, da masana, da kwararru, da masu sana'o'i, sun halarci shirye-shirye 20, inda suka nuna nasarorin da suka cimma a fannin kirkire-kirkire, tare da tattauna sassan hadin gwiwa tsakanin su.

Manyan kamfanonin dake kerawa, da masu hada-hadar cinikayyar na'urorin fasahar sadarwa kamar su Apple, da Alibaba, da Huawei, sun halarci taron, tare da gabatar da sabbin fasahohin su.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China