Jiya Litinin ne, aka bude babban taron kiyaye muhalli na MDD karo na 3 a hedkwatar shirin kare muhalli na MDD, wato UNEP a takaice da ke birnin Nairobin kasar Kenya. A yayin taron mai take 'kafa duniyar da babu gurbatar muhalli', za a mai da hankali kan batun gurbata muhalli, da kokarin cimma muhimman kudurori da dama, kana da yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakan gaggawa da suka dace don tinkarar kalubalen muhalli. A lokacin taron, matakan da wasu kamfanonin kasar Sin suke dauka na tinkarar matsalar gurbata muhalli na jawo hankulan jama'a sosai.
Yanzu, ga karin bayanin da wakiliyarmu Bilkisu ta hada mana.