in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar OAPEC na son hada hannu da Bankin Duniya a bangaren makamashi da iskar gas
2017-12-04 09:45:20 cri
Kungiyar kasashen Larabawa masu arzikin man fetur OAPEC, ta ce tana son hada hannu da bankin duniya a bangarorin makamashi da iskar gas.

Sakatare Janar na kungiyar Abbas Naqi, ya ce wakilan bankin duniya sun kai ziyara hedkwatar kungiyar dake birnin Kuwait a makon da ya gabata, inda suka tattauna kan cinikin iskar gas a yankin da kuma kasuwar lantarki ta bai daya na kasashen Larabawa.

Abbas Naqi ya ce wakilan sun jadadda rawar da OAPEC ke takawa a matsayin dandalin tattaunawa, yayin da suke bayyana rawar da bankin da kungiyar kawancen kasashen Larabawa wato Arab Leaque ke takawa ga kasuwar lantarki ta bai daya na Larabawa.

Ya ce ana sa ran gudanar da wasu tarukan da nufin mayar da burukansu zuwa managartan matakai.

Kungiyar OAPEC ta kunshi kasashen da suka hada da Iraqi da Kuwait da Libya da Saudiyya da Algeria da Bahrain da Masar da Qatar da Syria da Tunisia da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China