in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da a kulla sabuwar dangantaka tsakanin jam'iyyun duniya
2017-12-03 17:50:52 cri

A yau Lahadi, aka rufe taron manyan jami'an Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da na sauran jam'iyyu daban daban na duniya, wanda ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin. Manyan kusoshi mahalarta taron sun zartas da Shawarar Beijing, inda aka yi kira ga jam'iyyu daban daban da su kara amincewar juna, da musayar ra'ayi, da kokarin hadin gwiwa, don kafa wata sabuwar dangantaka tsakaninsu, irin na neman samun ra'ayin bai daya, da girmama juna, da kokarin koyi da juna.

Taron da ya gudana a birnin Beijing shi ne taron manyan jami'ai karon farko da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kira tare da sauran jam'iyyun siyasa na kasashe daban daban, inda aka samu shugabannin jam'iyyu kimanin 300 na kasashe fiye da 120 da suka halarci taron.

A nasa bangare, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya halarci bikin bude taron a ranar 1 ga wata tare da gabatar da wani jawabi. Jawabin da ya gabatar ya yi matukar janyo hankalin mahalarta taron, wadanda ke ganin cewa, manufofin da shugaba Xi Jinping ya gabatar kamarsu "samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin duniya", da "shawarar ziri daya da hanya daya" sun riga sun shiga cikin zukatan mutanen duniya. Jami'an sun nuna niyyar kara mu'amala da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kokarin hadin gwiwa da ita a fannoni daban daban.

Yayin da tsohon firaministan kasar Italiya Romano Prodi, wanda ya halarci taron, yake hira da wakilin CRI, ya ce: "Na fi yarda da manufar da kasar Sin ta dauka ta girmama hakkin da ake da shi na samun al'adu daban daban, da hanyoyin neman ci gaba daban daban a duniyarmu, domin manufar ita ce wata kyakyyawar dabarar da za'a iya amfani da ita wajen samun ra'ayin bai daya. Littafin da shugaba Xi Jinping ya rubuta don takaita ra'ayinsa wajen kula da wata kasa, shi ma ya nuna wani sako mai muhimmanci, wato sanya al'adu daban daban na duniya su kasance tare, bisa yunkurin samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin duniya. Ta haka ne kawai, za a iya samun damar magance hargitsi da tashin hankali."

A nata bangaren, mamba ta kwamitin zartaswa na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Faransa kuma ministar harkokin waje ta kasar Madam Samarbakhsh Lydia, tana ganin cewa, shawarar samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin duniya zabi ne da ya fi dacewa wajen samun bunkasuwa a nan gaba. Ta kara da cewa,

"Muna da imanin cewa, wannan shawara za ta samar da dama mafi kyau ga bunkasuwar bil Adama a nan gaba. Game da ci gabanmu a nan gaba, ya kamata mu 'yan Adam mu guji yin takara da juna, mu kawo karshen yaki da juna, kana da warware matsalar rashin daidaito. Ya kamata mu dukufa kan kyautata zaman rayuwar jama'ar duniya, da gudanar da dukkan abubuwan da za su taimakawa ci gaban bil Adama. Muna da aniyar yin tattaunawa kan wannan shawara, da kuma bayar da gudummawarmu a wannan fanni."

Kyautata fasahar wata jam'iyya ta fuskar kula da wata kasa da sauran harkokin siyasa, shi ma ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a wajen taron na wannan karo. Inda mahalarta taron suka fi mai da hankali kan irin nasarorin da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta samu a wannan fanni, musamman ma a bangaren ladabtarwa, da yaki da cin hanci da rashawa. Dangane da batun, mamban kwamitin zartaswa na jam'iyyar ANC ta kasar Afirka ta Kudu, Zizi Kodwa, ya ce, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta zama abin koyi ga sauran jam'iyyun siyasa na kasashen duniya,"Aikin yaki da cin hanci da rashawa tamkar wata jarrabawa ce ga wata jam'iyya dake rike da ragamar mulki. Amma a wannan fanni ina tsammanin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta zame mana abin koyi. Domin tana kama dukkan jami'an da suka aikata laifi, ko da manya ne, ko da kanana. Yayin da sauran jam'iyyu na kasashe daban daban su kan kaucewa daukar makatai kan manyan jami'ai. Ya kamata dukkan jam'iyyun kasashe daban daban su yi koyi da manufar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, saboda tana kokarin dakile cin hanci da rashawa, ta hanyar sauya tunani da kuma daukar matakan magance matsalar na zahiri ."(Bello Wang/Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China