in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron yanar gizo na duniya karo na 4
2017-12-03 13:08:29 cri

A yau Lahadi da safe, aka bude taron yanar gizo na duniya karo na 4 a birnin Wuzhen dake lardin Zhejiang na kasar Sin, inda wakilai 1500 daga sassan duniya suka halarci taron. Taken taron na wannan karo shi ne, "raya tattalin arziki na yanar gizo, da sa kaimi ga bude kofa da more fasahohi, da kuma kafa tsarin bai daya na raya yanar gizo". Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wasikar taya murnar bude taron.

A gun taron, za a gabatar da rahoton raya yanar gizo na duniya na shekarar 2017, da kuma rahoton raya yanar gizo na kasar Sin na shekarar 2017, wadanda za su shaida yadda yanar gizo ke samun bunkasuwa a kasa da kasa, da kuma yanayin bunkasuwar yanar gizo da makomarta a kasar Sin. A yayin da ake gudanar da taron, za a gudanar da taron baje koli da ya shafi yanar gizo, inda manyan kamfanonin yanar gizo da sabbin kamfannonin kirkire-kirkire fiye da 400 za su halarci taron, inda za a shaida sabbin fasahohin zamani na yanar gizo na duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China