Wu ya ce, kayan tarihi da aka gada daga kaka da kakanni, suna bayyana nagartattun al'adu na bil'adama, kana, alamu ne na kasancwar al'adu iri daban-daban a duk fadin duniya. A 'yan shekarun nan, wasu kungiyoyin 'yan ta'adda da rikice-rikicen da suka barke sun kara lalata irin wadannan kayan tarihi a duniya, har ma wasu kungiyoyin 'yan ta'adda sun yi fasa-kwauri tare kuma da sayar da kayan tarihin don tattara kudade, aika-aikar da suka kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya, kana, raina wa al'adun kasashe ne.
Wu ya kara da cewa, kamata ya yi kasa da kasa su yi aiki kafada da kafada, domin daukar kwararan matakan katse hanyoyin da kungiyoyin 'yan ta'adda suka bi wajen fasa-kwaurin kayan tarihi, da kiyaye kayan tarihi musamman a yankunan da suke fama da rikice-rikice.(Murtala Zhang)