in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar OPEC da abokan huldarta sun amince su tsawaita lokacin rage yawan man da suke fitarwa zuwa karshen 2018
2017-12-01 11:03:24 cri
Kungiyar kasashen masu arzikin man fetur OPEC da abokan huldarta, sun amince su tsawaita yarjejeniyar rage yawan man da suke fitarwa har zuwa karshen 2018, wato an tsawaita da karin watanni 9 a kan yarjejeniyar da aka cimma a baya.

A cewar ministan makamashi da albarkatun karkashin kasa na Saudiyya Khalid Al-Falih, kasashe 24, sun yanke shawarar ci gaba da rage yawan man da suke fitarwa na ganga miliyan 1.8 a ko wacce rana har zuwa ranar 31 ga watan Decemban 2018.

An yanke matakin ne la'akari da hasashen manazarta, duk da cewa Rasha ta bayyana damuwa game da tsawaita yarjejeniyar.

A shekarar 2016 ne kasashen kungiyar OPEC, suka cimma yarjejeniyar rage yawan man da suke fitarwa cikin watannin shidan farko na bana, domin farfado da farashin man a kasuwar duniya. Yarjejeniyar ta kuma samu goyon bayan wasu kasashe 11 da ba sa cikin kungiyar.

A kuma watan Mayun da ya gabata ne kasashen suka amince da tsawaita yarejejeniyar zuwa karshen watan Maris din 2018.

Khalid Al-Falih ya ce kasarsa na aiki kafada da kafada da Rasha. Inda Ministan makamashin Rasha Alexander Novak, ya ce Rasha da kasashen OPEC sun na da manufa iri guda ta fuskar daidaita kasuwar man fetur. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China