in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya gana da mambobin kawancen manyan jami'an kasashen duniya
2017-12-01 10:10:08 cri

Jiya Alhamis a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da mambobin kawancen manyan jami'an kasashen duniya, wadanda suka zo kasar ta Sin daga ketare domin halartar dandalin kasa da kasa na shekarar 2017 da aka gudanar a hotel din Congdu dake birnin Guangzhou na kasar Sin, tsakanin ranar 28 zuwa 30 ga watan Nuwamban da ya gabata, inda shugaba Xi ya bayyana cewa, "Ina farin ciki matuka da ganin ku a nan, saboda dukkanku tsoffin abokai ne, ko sabbin abokai, kuna mai da hankali sosai kan yanayin da kasar Sin ke ciki, kana ina son bayyana muku babbar godiya saboda kokarin da kuke yi domin sa kaimi kan ci gaban huldar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya."

A yammacin jiya a babban dakin taron jama'a dake nan Beijing, shugaba Xi ya yi ganawa da mambobin kawancen wadanda ke kunshe da tsohuwar shugabar kasar Latvia, kuma shugabar kawancen manyan jami'an kasashen duniya Vaira Vike-Freiberga, da tsohon firayin ministan kasar Italiya, kuma tsohon shugaban kwamitin tarayyar Turai Romano Prodi, da tsohon babban sakataren MDD Ban Ki-moon, da tsohon shugaban tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo da sauransu.

Tsohuwar shugabar kasar Latvia kuma shugabar kawancen manyan jami'an kasashen duniya Vaira Vike-Freiberga ta gaya wa shugaba Xi cewa, makasudin zuwansu nan kasar Sin shi ne kara fahimtar manufofin kasar Sin, inda ta bayyana cewa, "Muna da babbar sha'awa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashenmu da kasar Sin, mu ma muna mai da hankali matuka kan cudanyar dake tsakaninmu. Muna ganin cewa, kasar Sin tana kara taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya, shi ya sa al'ummun kasashen duniya suke fatan za su iyar kara fahimtar ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin kan al'amurran dake shafar kasa da kasa, da kuma manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa domin samun ci gaba."

Yayin ganawar, Xi ya yi bayani kan manufofin kasar Sin gare su, musamman ma kan manyan tsare-tsaren raya kasa da aka tsara yayin babban taron wakilan JKS karo na 19, inda ya ce, "Yayin taron, an fitar da manufofin raya kasa a fannonin tattalin arziki da siyasa, da al'adu da zaman takewar al'umma, da kiyaye muhallin halittu masu rai, da marasa rai da sauransu. Kana an gabatar da sabon tunanin raya kasa ta hanyar da ta dace; misali kirkire-kirkire, da sulhuntawa, da bude kofa da cimma moriyar juna da kuma kiyaye muhalli. Nan gaba kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje, domin cimma burinmu na samar da wadata ga dukkan al'ummar kasar mu yadda ya kamata."

Xi ya ci gaba da cewa, hanyar raya kasar Sin da ta dace, ita ce nacewa tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar, kasar Sin ta tsai da kudurin nan ne domin al'ummun kasar suka yi wannan zabe, ya sake jaddada cewa, har kullum kasar Sin tana ganin cewa, dole ne al'ummun kasashen duniya su zabi hanyar raya kasarsu da kansu.

Game da ra'ayin da kasar Sin ke dauka kan batun tafiyar da harkokin kasa da kasa, Xi ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna kwazo da himma kan kafa sabon tsarin kasa da kasa, domin cimma burin tabbatar da al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo shi ma ya yi jawabi a yayin ganawar, inda ya bayyana cewa, "A cikin rahoton da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin babban taron wakilan JKS karo na 19, ya bayyana kalmar sabon zamani, ina tsammanin cewa, kasar Sin za ta kara samun wadata a sabon zamani, kana sauran kasashen duniya su ma za su samu ci gaba a sabon zananin da muke ciki, kuma yanzu haka muna mai da hankali sosai kan shawarar ziri daya da hanya daya, kasancewar shawarar za ta kawo tasiri mai zurfi ga ci gaban kasashen Afirka."

An kafa dandalin kasa da kasa na Congdu ne a shekarar 2014, inda manyan jami'an kasashen duniya da aka gayyata, su kan tattauna kan batutuwan da suka fi jawo hankulan al'ummun kasashen duniya a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu da sauransu. Babban taken dandalin bana shi ne "tafiyar da harkokin kasashen duniya da manufofin kasar Sin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China