in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya yi kira da a dauki matakan yaki da cutar AIDS
2017-11-30 19:48:49 cri
Firaministan kasar Sin Li Kerqiang ya yi kira da a dauki matakan da suka dace na hana yaduwar cutar kanjamau da ma kula da wadanda ke fama da cutar, a wani mataki na gina kasa mai koshin lafiyar al'umma.

Li wanda ya bayyana hakan gabanin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya karo 30 da za a yi bikinta gobe Jumma'a, ya ce cutar kanjamau ta kasance alakakai ga rayuwar al'umma, don haka hana yaduwarta da kuma kula da wadanda ke fama da cutar, wani muhimmin bangare ne a kamfel da ake na gina kasar Sin mai koshin lafiyar jama'a.

Firaministan na kasar Sin ya kuma yaba irin ci gaba da aka samu na rage yawan masu kamuwa da cutar, kana ya kuma umarci sassan gwamnati a dukkan matakai, da su kara zage damtse tare da kara zurfafa bincike a fannin hana yaduwa da kula da wadanda ke fama da cutar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China