in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 4
2017-11-30 09:34:20 cri
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ya bayyana cewa sojojin sun kashe mutane 4 da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne a lokacin wani samame a jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Sani Usman, kakakin rundunar sojin Najeriya ya ce, sun yi nasarar damke wani da ake zargin kwamandan kungiyar ne a ranar Talata, a lokacin da dakarun suka karade wasu kauyuka a arewacin kasar dake makwabtaka da dajin Sambisa, wanda ya taba zama babban sansanin horas da mayakan Boko Haram a Borno.

Usman ya ce, kwamandan kungiyar da suka cafke mai suna Amman Judee, yana fuskantar tuhuma a halin yanzu.

Ko a karshen makon jiya ma, sojojin Najeriyar sun hallaka mayakan Boko Haram 14 a jahar Borno a wani samame da rundunar ta kaddamar.

Dakarun Najeriya sun yi nasarar karya lagon mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram, kana sun fantsama mayakan daga babbar maboyarsu dake dajin Sambisa tun a farkon wannan shekara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China