in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da gasar fidda mafiya kwarewa a fasahar sana'a ta Afirka karo na 4 a Kenya
2017-11-29 11:12:24 cri

Kwanan baya, kamfanin AVIC INTERNATIONAL na kasar Sin, da ma'aikatar ilmi ta kasar Kenya, sun kaddamar da gasar fidda mafiya kwarewa a fasahar sana'a ta nahiyar Afirka karo na 4, a birnin Nairobi.

A yayin gasar, an mai da hankali kan fasahar gine-gine, a kokarin taimakawa matasan wurin su kara samun aikin yi sakamakon ingantuwar fasahar sana'arsu.

Abokiyar aikinmu Tasallah Yuan dauke da karin bayani.

A yayin gasar da ake gudanar a wannan karo, an mai da hankali kan kyautata fasahar matasan Afirka ta fuskar gine-gine. Yanzu masu shiga gasar suna samun horo ne a wurin gina cibiyar ciniki ta duniya.

Zhao Leilei, darektan kula da cibiyar ba da misali kan yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Kenya ta fuskar ba da ilmin sana'a, wanda ke aiki a kamfanin AVIC INTERNATIONAL ya bayyana a yayin bikin kaddamar da gasar,"A gasar da ake gudanar a wannan karo, mun mai da hankali kan ayyukan gine-gine. Saboda aikin gine-gine yana bunkasa yadda ya kamata a Kenya a halin yanzu, kuma ana fuskantar makoma mai kyau. A bana, za mu gane wa idonmu yadda masu shiga gasar suke kyautata fasaharsu ta gine-gine. Sa'an nan kuma, za su samu kudin alawus da dama a lokacin gasar."

Margaret mai shekaru 24 a duniya ta shiga gasar a bana. Ko da yake matashiya ce, amma tana takara da maza a fannin ayyukan gine-gine. Ta bayyana fatanta na kara koyon fasaha, da zummar samun aikin yi mai kyau, inda ta ce,

"A baya, na taba koyon fasahar injiniyan lantarki, daga baya na fara sha'awar gine-gine, musamman ma bayan da na fara karatu a nan, na kara sha'awar fasahar gine-gine. Ina matukar farin ciki da samun irin wannan dama. Za a bai wa wadanda suka ci gasar guraben aikin yi. Dole ne na lashe gasar! Tabbas zan lashe gasar!"

A kasar ta Kenya, akwai yawan matasa kamar yadda Margaret take, wadanda suke fatan samun aikin yi cikin gajeren lokaci sakamakon kokarin da suke bayarwa. Amma babu dama da yawa kamar yadda suke fata. Kenya na fatan raya masana'antunta, ba injunan zamani kawai ba take bukata, har ma ba ta da isassun ma'aikata masu fasaha. A matsayinsa na wani kamfanin da yake hada kai da sassa daban daban masu ruwa da tsaki na Kenya cikin shekaru 20 ko fiye da haka, kamfanin na AVIC INTERNATIONAL, yana kokarin sauke nauyin da aka dora masa ta fuskar zamantakewar al'ummar kasa, ya bai wa matasan wurin damar samun guraben aikin yi, wanda kuma shi ne ainihin burinsa na shirya wasu harkokin ba da ilmi ta fuskar fasahar sana'a, ciki had da gasar fid da mafiya fasahar sana'a. Zhao Leilei ya gaya mana cewa, "Baya ga samun kudi, wajibi ne kamfanoni su taimaka wa mahukuntan wurin, musamman ma matasa. A shekaru 6 zuwa 7 da suka wuce, a kalla matasan wurin dubu 15 sun samun horaswa da muka gabatar. Sun samu fasahar sana'a, wadda take taimaka musu samun aikin yi, ta yadda yawan marasa aikin yi a kasar ta Kenya ya ragu."

Kamar yadda tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan ya fada, kamata ya yi matasa su kara sanin sauyin duniya da aikin kirkire-kirkire, kana kuma, ya kamata a tabbatar da ganin dukkan matasa sun samu damar shiga harkokin zaman al'ummar kasa. Gasar fid da mafiya fasahar sana'a ta Afirka, wata kyakkyawar dama ce ga matasan wurin.

Dinah J.C. Mwinzi, babbar sakatariyar sashen ba da horo ta fuskar fasahar sana'a karkashin shugabancin ma'aikatar ilmi ta kasar Kenya ta yaba wa gasar sosai, wadda ta taimaka sosai wajen samun aikin yi a wurin. Ta yi fatan cewa, za a ci gaba da gudanar da irin wannan gasa. "Ana bukatar fasahar sana'a wajen raya tattalin arzikin Kenya. Ina fatan wadanda suka shirya gasar fid da mafiya kwarewa a fasahar sana'a ta Afirka za su kara shirya irin wannan gasa a wasu fannoni."

Za a gudanar da zagayen karshe na gasar a ranar 8 ga wata mai zuwa, inda za a fid da mutum 24 mafiya kwarewa a fasahar ta gine gine. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China