in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin kasar Sin ya sanya takardar lamuni na kare sauyin yanayi cikin takardar RMB a Turai
2017-11-29 10:54:35 cri
An sanya takardar lamuni na kare sauyin yanayi da Bankin kasar Sin ya bayar a karon farko cikin jerin hada hadar musayar kudi ta Turai.

Shugaban reshen bankin kasar Sin dake birnin Paris Pan Nuo, ya ce Bankin ya yi nasarar bada lamunin ne a ranar 15 ga wannan wata cikin kashi uku da suka hada da Euro miliyan 700 da Dala miliyan 500 da kuma Yuan biliyan 1. Yayin da darajar takardar bukatar laumin ta karu da sama da sau 2.6

Pan Nuo ya ce takardun na aikin kare sauyin yanayi ne da suka hada da samar da tashohin lantarki daga iska da sauransu.

Jakadan kasar Sin a Faransa Zhai Jun, ya ce sanya wannan lamuni cikin kasauwar musayar kudi ta Turai na da ma'ana ta musamman, inda ya ce zo a lokacin da ake gaba da cika shekaru 2 da cimma yarjejeniyar Paris da kuma ziyarar da shugaban Faransa Emmanuel Macron zai kawowa kasar Sin.

Zhai ya kara da cewa, ya yi imanin cewa kasar Sin da Faransa na da dimbin damarmaki na karfafa dangantakarsu daga bangaren ayyukan ci gaba masu dorewa da harkokin kudi. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China