in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci OPCW da ta gaggauta lalata makamai masu guba na Japan dake sassan kasar Sin
2017-11-29 10:07:42 cri

Mahukuntan kasar Sin sun yi kira ga hukumar dake yaki da bazuwar makamai masu guba ta kasa da kasa ko OPCW a takaice, da ta mai da hankali ga aikin lalata makamai masu guba da kasar Japan ta yi watsi da su a wasu sassa na kasar Sin.

Wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar ta OPCW Wu Ken ne ya yi wannan kira, yayin taron kasashe mambobin hukumar karo na 22. Mr. Wu ya ce, duba da cewa kwance irin wadannan makamai na kasar Japan dake Sin na cikin muhimman ayyukan hukumar ta OPCW, rashin aiwatar da hakan tamkar watsi ne da muhimmin nauyi dake wuyan hukumar.

Ya ce, an gano irin wadannan makamai masu guba da Japan ta binne a kusan wurare 90 dake lardunan kasar Sin 17. Kuma duba da cewa an gano su ne ba tare da samun bayanai daga kasar ta Japan ba, tasirin su na iya shafar lafiyar al'umma, tare da kawo illa ga muhalli.

Game da burin hana yaduwar makamai masu guba kuwa, Mr. Wu ya sake jaddada cewa, kasancewar Sin ta fuskanci tasirin wadannan makamai a tarihin ta, kasar na fatan ganin an dakile amfani da su, bisa ko wane irin dalili a kuma kan ko wace kasa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China