in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta tura tawagar jami'an lafiya ta 15 Botswana
2017-11-29 09:54:29 cri

Kasar Sin ta cimma matsaya za ta tura tawagar jami'an kiwon lafiya ta 15 zuwa kasar Botswana.

Jakadan kasar Sin a Botswana Zhao Yanbo da ministan lafiya na kasar Botswana Wellness Dorcas Makgato ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin kasashen biyu.

Bisa tsarin yarjejeniyar, kasar Sin ta amince za ta tura tawagar jami'an lafiyar ta 15 zuwa Botswana domin su maye gurbin tawagar jami'an kiwon lafiyar ta 14 da ta kammala aikinta a kasar.

Da yake jawabi a lokacin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar, Zhao ya bayyana cewa, hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya muhimmin al'amarin a tsakanin kasashen biyu. Tawagar jami'an kiwon lafiya ta kasar Sin ta ba da gagarumar gudunmowa ga hadin gwiwar kasa Sin da Botswana.

Zhao ya bayyana kyakkyawar fata cewa, sabbin likitocin tawagar kiwon lafiyar da za'a tura, za su martaba tsarin al'adun jama'ar kasar, kana za su kiyaye ka'idojin aikinsu bisa ga tanade tanaden dokokin tsarin kiwon lafiya na kasar Sin da na kasa da kasa domin ba da taimakon gaggawa don inganta lafiyar jama'ar kasar ta Botswana.

A nasa bangaren, Magkato, ya yabawa gwamnatin kasar Sin sakamakon dukkan taimakon da take baiwa kasar ta Botswana cikin shekaru masu yawa da suka gabata, musamman a lokutan da kasar ke cikin tsananin bukatar taimako.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China