in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin raya kasashe masu tasowa a birnin Antalya na Turkiya
2017-11-28 13:50:16 cri
Jiya Litinin ne, aka bude bikin baje kolin raya kasashe masu tasowa na shekarar 2017 a birnin Antalya na kasar Turkiya. Babban taken taron na wannan karo shi ne "Hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa a yayin da ake samun manyan sauye-sauye a fadin duniya", inda aka nuna kyawawan sakamakon da aka samu da kuma abubuwan da aka yi bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa cikin sabon zamani.

Manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da harkokin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kana shugaban ofishin kula da harkokin hadin gwiwar kasashe masu tasowa na MDD Jorge Chediek ya bayyana a yayin bude bikin baje kolin cewa, bikin baje kolin raya kasashe masu tasowa na kasa da kasa ya samar da wani dandali ga kasashe masu tasowa, inda za su iya yin mu'amala kan fasahohin neman ci gaba da kuma samar da karin damammakin yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Haka kuma, ba kawai kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki za su ba da gudummawa ga bunkasuwar kasa da kasa ba, har ma kasashen dake fama da karancin ci gaba.

Bikin baje kolin na kwanaki 4, zai mai da hankali ne kan bunkasuwar kimiyya da fasaha, samar da guraben aikin yi ga matasa, raya harkokin gona da dai sauransu, watau fannin da kasashe masu tasowa suka saba yin hadin gwiwa a tsakaninsu.

Haka zalika, za a tattauna batun sabbin fannonin raya hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, kamar sabunta tsarin gudanar da harkokin siyasa, harkar jin kai da neman ci gaba, kiyaye zaman lafiya da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China