in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da taron koli na kungiyar AU da ta EU karo na 5
2017-11-28 10:31:49 cri

A ranar 29 ga wannan wata ne za a gudanar da taron koli na kungiyar AU da ta EU karo na 5 a birnin Abidjan dake kasar Cote d'Ivoire, an gudanar da wannan taron karon da ya gabata ne a nahiyar Afirka a shekaru 7 da suka wuce.

Manazarta sun yi nuni da cewa, bisa yanayin gaza warware rikicin 'yan gudun hijira a nahiyar Turai, taron kolin zai samar da wani muhimmin dandalin yin shawarwari a tsakanin kungiyar AU da ta EU, wadanda za su hada kai wajen tinkarar kalubale tare.

Bisa kididdigar da kwamitin shirya taron koli na kungiyar AU da ta EU ya yi, an ce, an gayyaci shugabannin kasashen Afirka da Turai fiye da 10 da su halarci taron. Ana kuma sa ran cewa, mutane fiye da 5000 za su halarci taron, kana tawagogin kasashen da suke sada zumunta da kungiyoyin biyu da hukumomin kasa da kasa za su halarci taron.

Ana gudanar da taron koli na kungiyar AU da ta EU a kasashen Afirka da Turai bisa tsarin karba karba. A bana, za a gudanar da taron kolin a nahiyar Afirka. Wannan ne karo na 3 da aka gudanar da taron a Afirka, kana wannan ne karo na farko da za a gudanar da shi a yankin kudu da hamadar Sahara na Afirka.

Za a gudanar da taron kolin a wannan karo bisa yanayin barkewar rikicin 'yan gudun hijira a nahiyar Turai a shekarar 2015. 'Yan gudun hijira daga yankin gabas ta tsakiya da nahiyar Afirka sun shiga nahiyar Turai, wanda hakan ya kawo matsin lamba ga nahiyar Turai, kana ya kawo illa ga nahiyar Turai a fannin zaman lafiya da rayuwar jama'a, don haka a kan ki karbar 'yan gudun hijira. Batun 'yan gudun hijira ya sa kaimi ga nahiyar Turai da ta yi la'akari da manufofin taimakawa nahiyar Afirka. Alal misali kasar Jamus ta gabatar da shirin Marshall irin na nahiyar Afirka, wato shirin farfado da nahiyar Afirka, inda ake sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin Afirka, da samar da ayyuka ga matasan Afirka don hana 'yan gudun hijira na Afirka su shiga nahiyar Turai.

Manazarta na ganin cewa, batutuwan 'yan gudun hijira, da kiyaye tsaro, da dangantakar dake tsakanin Afirka da Turai, za su zamo manyan batutuwan da za a tattauna a gun taron kolin a wannan karo.

Taken taron kolin a wannan karo shi ne "zuba jari ga bangaren horar da matasa don samar da kyakkyawar makoma mai dorewa". Manazarta na ganin cewa, Afirka da Turai suna fuskantar kalubale tare a fannin bunkasa rayuwar matasa, don haka za a mai da hankali kan wannan batu a taron kolin.

A shekarun baya baya nan, kungiyar AU ta dora muhimmanci kan batun ba da ilmi, da samar da ayyukan yi ga matasa. A gun taron koli na kungiyar AU karo na 28, da na karo na 29 da aka gudanar a watan Janairu da ta Yuni na bana, takensu na da nasaba da batun matasa. Shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki ya bayyana cewa, matasa su ne muhimmin albarkatun nahiyar Afirka, kuma biyan bukatun matasan Afirka zai samar da kyakkyawar makoma gare su.

Matsalar matasa ita ma ta kasance a nahiyar Turai. An ce, koda yake, an farfado da tattalin arzikin nahiyar Turai, amma matsalolin rasa guraban aikin yi, da yaki da talauci, da matsalar rashin daidaito da ake samu yayin da rikicin hada-hadar kudi ya barke su ma suna addabar nahiyar.

A sakamakon gudanar da taron kolin a wannan karo, kasar Cote d'Ivoire ta kara jawo hankalin kasa da kasa.

A shekarar 2002, an yi juyin mulki a kasar Cote d'Ivoire, ko da yake ba a cimma nasarar juyin mulkin ba, amma an ta da yakin basasa a kasar. A shekarar 2010, bayan da aka gama zaben shugaban kasar, rikicin siyasa ya barke a kasar. Hargitsin ya haifar da babbar illa ga bunkasuwar kasar.

Amma yanzu, an farfado da kasar Cote d'Ivoire, an kuma bunkasa tattalin arzikinta cikin sauri, wadda ta kasance sabuwar kasa mafi samun ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afirka, kana kasar tattalin arziki mafi girma ta kawancen tattalin arziki da hada hadar kudi a yammacin Afirka. Kaza lika kuma kasa ta biyu mafi girma a fannin tattalin arziki ta kungiyar ECOWAS.

Har ila yau Cote d'Ivoire tana daya daga cikin manyan kasashen da suka fi samun bunkasuwar tattalin arziki a duniya. A cikin shekaru 5 da suka gabata, yawan tattalin arzikin kasar na karuwa da kashi 9 cikin dari a kowace shekara, wadda ta kasance kasa ta biyu a wannan fanni a nahiyar Afirka. Kana kasar na kan gaba wajen fitar da Coco, da kwallon cashew, da roba, da albarkatun giginya ga sassan duniya daban daban.

A daya hannu kuma Cote d'Ivoire ta dora muhimmanci ga manufofin diplomasiyya a tsakaninta da sauran kasashen duniya, ta taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban a duniya. Ta mai da aikin gudanar da taron kolin a wannan karo a matsayin abin yabo, inda ta sanar da cewa, hakan ya shaida irin yadda ta sake koma dandalin duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China