in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An fidda tsari game masana'antu da yanar gizo
2017-11-28 09:24:49 cri

Mahukuntan kasar Sin sun fidda wani tsari na bunkasa manufar hade sassan masana'antun kasar da yanar gizo ko internet, a wani mataki na bunkasa ci gaban masana'antu.

Majalissar zartaswar kasar ce ta tabbatar da hakan, tana mai bayyana tsare tsaren da za a aiwatar domin cimma wannan buri. Karkashin manufar ana fatan nan da shekarar 2025, za a kai ga kammala hade dukkanin yankunan kasar da hidimar sadarwar yanar gizo.

Kaza lika ana fatan nan da shekarar 2035, kasar ta Sin za ta zamo a sahun gaba, wajen cin gajiyar hidimar masana'antu masu hade da internet.

Da yake karin haske game da tasirin hakan, mataimakin ministan masana'antu da fasahar sadarwa Chen Zhaoxiong, ya ce habaka wannan fanni na da matukar muhimmanci, musamman a gabar da ake fuskantar karin takara tsakanin sassan masana'antu na kasa da kasa.

Karkashin wannan manufa dai mahukuntan kasar Sin na da burin gudanar da ayyuka da suka hada da kara saurin hidimar yanar gizo, da rage kudin hidimar, da tsara ka'idojin amfani da internet. Sauran sun hada da kafa cibiyar kirkire kirkire, da kara inganta tsaron internet. Har ila yau za a samar da daidaito tsakanin kasuwanni, da karin kudaden aiwatar da manufar yadda ya kamata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China