in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Tanzania ya jinjinawa hidimar jinya da jirgin ruwa na sojojin ruwan kasar Sin mai suna Peace Ark ya bayar
2017-11-27 12:22:37 cri

A ranar 26 ga wata, jirgin ruwa dake ba da hidimar jinya mai suna "Peace Ark" na sojojin ruwan kasar Sin ya bar tashar jiragen ruwa ta birnin Dar es Salaam, hedkwatar mulkin kasar Tanzania, bayan da ya kammala aikin ziyarar kasar ta kwanaki takwas. Kafin tashin jirgin, shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya shiga cikinsa don ganewa idanunsa na'urorin ba da jinya, ya kuma gai da masu aikin jinya.

A yayin bikin ban kwana da wannan jirgi, shugaba Magufuli ya bukaci jakadar kasar Sin da ke Tanzaniya madam Wang Ke, da Manjo Janar Guan Bolin mai kula da aikin ba da tallafin kiwon lafiya na jirgin ruwa na Peace Ark na shekarar bana, da su mika wasikar da ya rubuta ga shugaba Xi Jinping. A cikin jawabin da shugaba Magufuli ya bayar, ya nuna matukar godiya ga gwamnatin kasar Sin da ta tura jirgin ruwa na Peace Ark zuwa kasar Tananiya. Bugu da kari kuma, ya yi fatan jirgin zai iya sake zuwa kasarsa don kara ba da hidimar jinya ga jama'arsa. Shugaba Magufuli yana mai cewa,

"A madadin gwamnatin kasar Tanzaniya, ina nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, da ta aiko da jirgin ruwa mai ba da tallafin kiwon lafiya zuwa kasar Tanzaniya. Na gamsu da aikin hidima da jinya da kuka baiwa marasa lafiyarmu. Yawan jama'ar kasata da kuka yiwa hidimar jinya ya zarce dubu shida, har abada ba za mu manta da taimakon da kuka ba mu ba. Kuwa wannan aiki ya bude wani sabon shafi ga dangantakar da ke tsakanin kasashenmu. Na gode!"

Wannan shi ne karo na biyu da jirgin ruwa na Peace Ark ya ziyarci kasar Tanzaniya ban da ziyararsa ta farko a shekarar 2010, wanda ya samu karbuwa sosai daga wajen mazauna wurin, don haka ne ma kimanin mutane 1000 suka halarci jirgin domin ganin likita a ko wace rana.

A ranar 24 ga wata, wani dan kasar Tanzaniya da ya kamu da cutar duwatsun mafitsara ya isa jirgin ruwa na Peace Ark don neman samun jinya, bayan da wani Basine mai aikin sa kai da ke iya harshen Swahili ya yi masa tafinta, Dr. Zhang Zhensheng mai kula da cututtukan da suka shafi mafitsara ya ba da shawarar cewa,

"A cikin mafitsararka, akwai wani dutse da girmansa ya kai kamar haka. Idan ba a kawar da shi cikin lokaci ba, to za ka rika yin fitsari mai jini. Yanzu shawarata ita ce, da farko ya kamata a kau da gyambon, a kuma dakatar da fitawar jini, sannan cikin gaggawa a yi maka tiyata."

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, yayin da jirgin ruwa na Peace Ark ke ziyartar Tanzaniya, ban da ba da jinya cikin jirgin, an kuma tura likitoci 74 zuwa asibitoci daban daban na birnin Dar es Salaam, don su yi hadin gwiwa tare da likitocin wurin wajen ba da jinya. Gaba daya dai an ba da jinya ga mutane 6441, kuma an yi bincike kan mutane a fannonin lafiyar jiki kamar na amfani da na'urar CT, da DR, da hoton binciken bugun zuciya da dai sauransu ga mutane 3917. Baya ga gyara na'urorin asibiti 26, da yin tiyata har sau 31.

Juma Bakari mai shekaru 67 da haihuwa ya taba yin karatu a wata jami'ar kasar Sin. Yanzu ya riga ya yi aiki har na tsawon shekaru 30 a matsayinsa na injiniya a kan layin dogo dake tsakanin Tanzaniya da Zambia. Yanzu haka ya iya Sinanci kadan. A wannan karo an kai shi jirgin ruwan don duba lafiyar jikinsa, ya kuma nuna godiyarsa sosai ga wannan aiki da Sinanci. Ya ce,

"Ina nuna godiya sosai ga abokanmu Sinawa, da likitoci Sinawa da suka zo Tanzaniya don ba mu taimako. Ina kuma godiya da zuwan jirgin ruwa na Peace Ark, mai ba da hidimar jinya ga kasarmu."

Daga ranar 26 ga watan Yuli na shekarar bana, jirgin ruwa da ke ba da taimakon jinya mai suna Peace Ark na sojojin ruwan kasar Sin, ya fara gudanar aikin ba da jinya a bana. Daya bayan daya kuma, ya ziyarci kasashen Djibouti, da Saliyo, da Gabon, da Jamhuriyar Kongo, da Angola, da Mozambique da kuma Tanzaniya, inda ya ba da hidimar jinya ta jin kai. Bayan da jirgin ya bar Tanzaniya, zai ratsa tekun Indiya, kuma ana sa ran zai isa kasar Timor-Leste da ke Asiya, don ziyara da ba da taimakon kiwon lafiya. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China