in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Somalia ya nada sabon ministan tsaro
2017-11-27 10:31:04 cri

Firaministan kasar Somalia Hassan Ali Khaire ya nada Mohamed Mursal Sheikh, a matsayin sabon ministan tsaron kasar, bayan da Abdirashid Abdullahi Mohamed ya yi murabus daga mukamin ministan tsaron kasar a watan Oktoba.

Sabon ministan tsaron shi ne jakadan Somalia a kasar Turkiyya na farko, tun bayan durkushewar gwamnatin Somalia har zuwa shekarar 2011, kana shi ne tsohon ministan albarkatun ruwa da makamashi na kasar ta gabashin Afrika.

Tsohon ministan tsaron na Somalia Abdirashid Abdullahi Mohamed ya yi murabus daga aiki ne a ranar 12 ga watan Oktoba, bayan da aka samu mummunan harin ta'addanci wanda ya hallaka jama'a masu yawa a kasar, da kuma rashin jituwa da aka samu tsakaninsa da tsohon babban hafsan sojojin kasar Somalia.

Ministan yada labarai na kasar Somalia Abdirahman Omar Osman, ya sheda wa 'yan jaridu a Mogadishu, babban birnin kasar cewa, Khaire ya kuma sallami ministan kula da al'amurran addinai na kasar Iman Abdullahi Ali.

Sai dai ministan yada labaran bai yi karin haske dangane da dalilan da suka sanya aka kori ministan al'amurran addinai na kasar daga mukaminsa ba. Ali shi ne minista na farko da aka sallama tun bayan da Khaire ya kafa majalisar ministocinsa a watan Maris.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China