in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a samar da jami'an sa ido na dindindin a makarantun renon yara dake Beijing
2017-11-27 10:23:45 cri

Mahukuntan birnin Beijing dake nan kasar Sin, sun bayyana kudurin su, na tabbatar da samar da jami'an sa ido na dindindin, a daukacin makarantun renon kananan yara dake birnin.

Hakan dai na zuwa ne bayan da aka samu zarge zarge na cin zarafin kananan yara, a daya daga irin wadannan makarantu na rukunin RYB dake gundumar Chaoyang dake birnin na Beijing, lamarin da ya jawo kiraye kiraye daga sassa daban daban, game da bukatar daukar matakan dakile wannan matsala.

A cewar hukumar dake lura da harkokin ilimi ta birnin na Beijing, za a rika lura da fannonin kayayyakin aiki, da na kaucewa hadurra, da tsaftar muhalli, da na gudanarwa a daukacin makarantun horas da kananan yaran.

Kaza lika za a tanaji sashen adana bayanai, game da sakamakon binciken da ake aiwatarwa, a kuma dauki matakan gyara a duk inda aka ga dacewar hakan.

A cewar hukumar, nan ba da dadewa ba za a gudanar da wani gagarumin shiri na binciken kwakwaf, game da kare lafiyar yara a daukacin makarantun renon dake birnin.

Ana fatan aiwatar da sauye sauye cikin gaggawa, a bangaren kare hadarin gobara, da fannin sanya ido ga kula da lafiya, da kuma na ciyar da yaran abinci a duk inda aka samu bukatar hakan.

Har ila yau an bukaci mahukuntan gundumomin dake birnin, da su dauki matakan karfafa hadin gwiwa tsakanin irin wadannan makarantu da bangaren iyayen yara, tare da samar da wata kafa ta daukar matakan ko ta kwana, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China