in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jigo a jam'iyya mai mulkin Afrika ta kudu ya bayyana fargabar ballewar jam'iyyun hadakar kasar
2017-11-27 10:02:47 cri

Sakatare janar na jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Afrika ta kudu Gwede Mantashe, ya yi gargadi game da yiwuwar ballewar jam'iyyun siyasar kasar 2 wato jam'iyyar SACP, da ta COSATU wadanda suka yi kawance da jam'iyya mai mulkin kasar.

Mantashe ya shedawa wakilan jam'iyyar ANC a lokacin wani taro da suka gudanar a yammacin lardin Cape dake garin Cape Town cewa, jam'iyyar ta ANC ba za ta taba laminta gamayyar jam'iyyun hadakar su balle ba.

An shirya taron ne da nufin tattara wakilan jam'iyyar ta ANC na yankunan 182 na kasar, gabanin gudanar da babban taron jam'iyyar wanda za'a gudanar a tsakiyar watan Disamba, inda a lokacin ne za'a zabi wanda zai gaji shugaba Jacob Zuma na kasar.

Mantashe ya nanata cewa, duk mutumin da aka zaba, dole ne ya farfado da martabar hadakar da jam'iyyar ta ANC ta yi da jam'iyyun SACP da COSATU.

Tun lokacin da ta dare madafun iko a shekarar 1994, jam'iyyar ANC tana shugabanci ne karkashin kawance da jam'iyyun SACP da COSATU. Sai dai a halin yanzu, wannan hadaka tana fuskantar barazanar wargajewa bayan da jam'iyyun na SACP da COSATU suka fara yin kiraye-kirayen neman shugaba Zuma ya yi murabus.

A watan Oktoba, Zuma ya tube Blade Nzimande, sakatare janar na jam'iyyar SACP daga mukamin ministan ma'aikatar ilmi mai zurfi na kasar, a lokacin wani garambawul da shugaban ya yi wa majalisar ministocinsa, matakin ya kara raunata kyakkyawar alakar gamayyar jam'iyyun 3.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China