in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya isa Hungary don halarta taron kawance tsakanin kasarsa da kasashen yankin Turai
2017-11-27 09:39:44 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya isa Hungary a jiya Lahadi domin ziyarar aiki da halartar taro karo na 6 na shugabannin gwamnatocin kasar Sin da kasashe 16 na tsakiya da gabashin Turai da za a yi a Budapest.

Firaministan Hungary Viktor Orban da wasu ministoci ne suka tarbi Li Keqiang a filin jirgin sama.

Da yake tsokaci game da cikar kawancen kasar Sin da kasashen na Turai shekaru 5, Li Keqiang ya ce, hadin gwiwar na ci gaba da fadada cikin shekaru 5 da suka gabata, inda al'ummomin yankunan biyu ke amfana daga sakamakon hadin gwiwar da muhimman ayyukan da aka aiwatar.

Ya ce, ba kadai taimakawa ci gaban kasashen tsakiya da gabashin Turai kawancen ya yi ba, har ma da inganta samar da daidaito ta fuskar ci gaba a baki dayan Turai, wanda ke da muhimmanci ga tsarin dinkewar nahiyar.

Firaministan ya ce, a shirye kasar Sin take ta yi aiki da dukkan bangarori wajen nazartar nasarorin da aka samu cikin shekaru 5 da suka gabata, tare da tsara manufofin da ake son cimmawa a nan gaba don samun dimbin nasarori. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China