in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministan kasar Sin ya nanata aniyar kasar ta hada kai da kasashen tsakiya da gabashin Turai
2017-11-26 13:46:44 cri
Firaiministan kasar Sin Li Keqiang ya nanata aniyar kasarsa na karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashe 16 dake tsakiya da kuma gabashin nahiyar Turai wato (CEEC) a takaice, da kuma daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasar Sin da ta Hungary zuwa wani babban mataki.

Mista Li ya bayyana hakan ne cikin wani sharhi wanda jaridar The Hungarian Times ta wallafa, gabanin halartar taron shugabannin gwamnatocin Sin da na CEEC, wanda ake fatan gudanar da shi tsakanin ranar 26 zuwa 29 ga watan Nuwamba a Budapest da kuma ziyarar aikin da zai kai kasar Hungary.

Da safiyar yau Lahadi ne firaiministan kasar Sin Li Keqiang ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasar Hungary don ziyarar aiki, kana zai halarci taron shugabannin gwamnatocin Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai wanda zai gudana a birnin Budapest.

Li, zai kuma halarci taron tattaunawa na majalisar shugabannin gwamnatoci (firaiministoci) karo na 16 na kungiyar hadin gwiwar Shanghai a birnin Sochi na kasar Rasha, tsakanin 30 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China