Li Keqiang, ya ce cibiyar ta bada gagarumar gudunmawa wajen raya bangarori masu zaman kansu, wanda ya zama tubalin daidaita tattalin arzikin kasar da samar da hanyar samun kudin shiga tare da taka muhimmiyar rawa wajen inganta fasahohi da ciyar da harkokin kudi da tattalin arziki gaba.
Firaministan ya bukaci cibiyar a dukkan matakai ta samar da ci gaba na bai daya a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu tare da inganta yanayin ciyar da bangarori masu zaman kansu gaba, domin tabbatar da samun karuwar hannayen jari a bangaren tare da raya sabon tsarin tattalin arziki.
Ya kara da cewa, ya kamata cibiyar ta kiyaye sabbin manufofin tattalin arziki yayin da take kokarin tabbatar da inganci da adalci da dorewarta tare da samar da ingantattun hidimomi a fannin kasuwanci.
Cibiyar raya masana'antu da cinikayya ta kasar Sin, da ta kunshi masana'antu da mutane daga bangarorin cinikayya da masana'antu masu zaman kansu, cibiya ce mai zaman kanta da aka kafa a shekarar 1953. (Fa'iza Mustapha)