Ministan cikin gidan kasar Noureddine Bedaoui ya sanar da cewa an samu fitowar masu kada kuri'u da kashi 33.26 bisa 100 a zabukan shugabannin kananan hukumomin, yayin da aka samu fitar masu kada kuri'a da kashi 34.46 bisa 100 na zabukan majalisar kansilolin yankunan kasar, yayin da ya rage sa'oi biyu a kammala zabukan.
A shekarar 2012, an samu fitowar masu kada kuri'un a zabukan shugabannin kananan hukumomin kasar da kashi 28 bisa 100, yayin da aka samu fitar masu kada kuri'a da kashi 27 bisa 100 na zabukan majalisar kansilolin yankunan kasar.
A nasa bangaren, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar, Abdelouahab Darbal, ya ce an samu kura-kurai sama da 600 a zabukan, sai dai ya ce basu shafi sahihancin yadda aka gudanar da zabukan ba.
Kimanin 'yan kasar Algeriyan miliyan 23 ne suka cancanci kada kuri'a a zaben tsakanin 'yan takara 165,000 wadanda zasu wakilci kananan hukumomi da majalisun dokokin yankunan kasar 1541. Sama da 'yan takara 16,000 ne suka fafata a zabukan kujerun majalisun dokokin kananan hukumomin kasar 48.
Kimanin jami'an 'yan sanda 180,000 aka tura yankunan kasar don sanya ido a zaben.(Ahmad Fagam)