A ranar 22 ga watan nan ne ministan tsaron kasar Turkiyya Nurettin Canikli ya sanar da cewa, an sallami janar din sojan kasar 150 daga bakin aikinsu, sakamakon samunsu da hannu cikin yunkurin juyin mulkin kasar da ya ci tura a watan Yulin shekarar 2016.
An labarta cewa, yayin da ake bin bahasin juyin mulkin, gwamnatin Turkiyya ta kama mutane fiye da dubu 50, ta kuma kori wasu dubu 150 daga mukamansu, wadanda yawancinsu suka fito daga hukumomin 'yan sanda, da rundunar soja, da hukumomin zartas da dokoki, da na leken asiri, da hukumomin gwamnati, da makarantu. (Tasallah Yuan)