in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mugabe ya sanar da yin murabus
2017-11-22 11:21:45 cri

A jiya Talata ne, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, lamarin da ya kawo karshen shekaru 37 da ya shafe yana shugabancin kasar Zimbabwe.

A yammacin jiya ne, yayin da majalisar dokokin kasar Zimbabwe ke tattauna batun shugaba Mugabe, shugaban majalisar wakilai ta kasar Zimbabwe Jacob Mudenda ya dakatar da taron tare da sanar da cewa,

"Na dakatar da taron da ake gudanarwa a yanzu, domin na sanar da ku cewa, bisa aya ta 96 sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin kasar, na samu wata wasika daga fadar shugaban kasar, wadda ke cewa …"

Bisa kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe, idan shugaban kasa yana son yin murabus, ya kamata ya mika takardar yin murabus ga shugaban majalisar dokokin kasar. Bayan da shugaban majalisar dokokin kasar ya karbi takarda, nan da nan zai gabatar da wannan sako a fili. Don haka, yayin da shugaban majalisar dokokin kasar ya bayyana hakan, membobin majalisar dokokin kasar sun fahimci abin da ke faruwa da kuma abin da aka bayyana a cikin wasikar. Daga nan aka barke da tafi da shewa a wurin har na tsawon mintoci biyu ko fiye, wanda ya dakatar da maganar Mudenda. Bayan da aka yi shiru, sai Mudenda ya karanta wasikar yin murabus da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya aike.

"Ni, Robert Mugabe, na yi murabus daga mukamin shugaban kasar Zimbabwe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada ba tare da bata lokaci ba"

A cikin wasikar, Mugabe ya bayyana cewa, ya tsaida wannan kuduri ne bisa radin kansa, tare da fatan za a mika mulki cikin lumana. Daga baya, aka sake barkewa da shewa a majalisar. Shugaban majalisar dokokin kasar ya sanar da cewa, majalisa ta dakatar da taron da ta shirya saboda shugaba Mugabe ya sanar da yin murabus da kansa, Bayan taron, babban mai tsawarawa a majalisa dan jam'iyyar ZANU-PF dake kan mulkin kasar Lovemore Matuke ya bayyana cewa, yana taya jama'ar kasar Zimbabwe farin ciki sosai. Ya ce,  

"Ban yi mamaki wasikar murabus da Mugabe ya aike a yau ba. Domin yana fuskantar matsin lamba sosai. Fiye da kashi 92 cikin dari na membobin majalisar dokokin kasar ciki har da membobin jam'iyyar dake mulkin kasar da na jam'iyyar adawa sun tsaida kudurin jefa kuri'un tsige shi daga mukaminsa. Yanzu ina farin ciki sosai, haka ma jama'ar kasar su ma suna farin ciki sosai."

Jama'a da dama ne suka taru a wajen majalisar, don murnar samun labarin murabus din da Mugabe ya yi. Amma wasu mutane suna da bambancin ra'ayi, wani mutum ya bayyana cewa,  

"Shi ne jagoranmu a cikin shekaru 37 da suka gabata, a hakika ya yi kuskure, amma bai kamata ya sauka daga mukaminsa ta irin wannan hanya ba. Shi alama ce a nahiyar Afirka, ya kamata ya sauka daga mukami ta wata hanya mafi dacewa, inda ya gama wa'adinsa na wannan karo, sai ya sauka bayan zaben shugaban kasar da za a yi a badi."

Daga baya, jam'iyyar ZANU-PF za ta mika takarda ga majalisar dokokin kasar, inda ta nada sabon shugaban kasar. Mr Matuke ya kara da cewa,

"Kafin hakan, mun riga mun zabi Emmerson Mnangagwa a matsayin shugaban jam'iyyar Zanu-PF kuma babban sakataren jam'iyyar. Bisa kundin tsarin mulkin kasar, za a mika wasika ga shugaban majalisar dokokin kasar, inda za a bukace shi da ya nada shi a matsayin shugaban kasar na wucin gadi. Na yi imani cewa, nan da sa'o'i 48 za a nada sabon shugaban kasa." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China