in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a kwantar da hankali a Zimbabwe biyo bayan murabus na shugaban kasar
2017-11-22 11:05:09 cri
MDD ta yi kira da a zauna lafiya tare da kai zuciya nesa a Zimbabwe, biyo bayan murabus na shugaba Robert Mugabe, da ya shafe shekaru 37 ya na jan ragammar mulkin kasar tun bayan da ta samu 'yancin kai.

Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres da shugaban babban zauren Majalisar Miroslav Lajcak, dukkansu sun yi kira da a zauna lafiya tare da kai zuciya nesa a kasar dake kudancin nahiyar Afrika da aka shafe mako guda ana fuskanatar takaddamar siyasa.

Shugaban majalisar dokokin Zimbabwe Jacob Mudenda ne ya sanar da murabus din na Mugabe a jiya Talata, kwana guda bayan shugaban mai shekaru 93 ya yi watsi da wa'adin da jam'iyyarsa ta bashi na ya yi murabus.

A makon da ya gabata ne sojojin kasar suka yi wa Mugabe daurin talala bayan ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa. Jam'iyyar tasa ce kuma ta dawo da Mnangagwa tare da neman Mugabe ya yi murabus.

Bayan Mugabe ya ki ba da kai ne jam'iyyar ta yi barazanar tsige shi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China