in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji sun fatattaki mayakan IS baki daya, in ji firaministan kasar Iraki
2017-11-22 11:04:51 cri
Firaministan kasar Iraki, Haider al-Abadi ya ce, sojojin kasar sun yi nasarar fatattakar mayakan kungiyar IS baki daya.

Abadi ya bayyana yayin wani taron manema labarai da aka shirya jiya Talata cewa, Iraki ta samu dimbin nasarori a yakin fatattakar 'yan ta'adda a cikin shekaru uku da suka wuce. Ragowar mayakan na IS dai sun buya a yankunan hamada dake yammacin kasar ta Iraki bayan da sojoji suka kwace garin Rawa.

Ya ce, nan gaba kadan zai sanar da galaba ta karshe da aka samu kan mayakan na IS bayan da sojojin gwamnatin kasar suka kawo karshen matakan soja da suke dauka a yankunan hamada dake yammacin kasar.

Abadin ya kuma jaddada cewa, har yanzu kungiyar 'yan ta'adda na ci gaba da kawo barazana ga bil'adama, kuma yadda za'a hana IS kaddamar da hare-hare a cikin birane da garuruwa shi ne babban kalubalen dake gaban hukumomin tsaron kasar Iraki.

A shekara ta 2014 ne, kungiyar IS ta kwace yankuna da dama dake arewaci da yammacin kasar Iraki. Bayan da aka shafe tsawon shekaru uku ana yaki da su, dakarun gwamnatin kasar sun kwace ikon da akasarin yankunan dake hannun IS. A ranar 17 ga watan da muke ciki, sojojin gwamnatin Iraki suka yi nasarar karbe ikon garin Rawa, matattarar karshe ta kungiyar IS a kasar Iraki. A halin yanzu sojojin na ci gaba da fatattakar mayakan IS a yankin hamada dake yammacin jihar al-Anbar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China