in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Casablancan Morocco zai karbi bakuncin makon cinikayya na kasar Sin na farko
2017-11-22 10:50:21 cri
A karon farko birnin Casablanca kana cibiyar harkokin kasuwancin kasar Morocco zai karbi bakuncin makon cinikayya na kasar Sin, wanda zai gudana daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Disamba mai kamawa.

Da take tabbatar da hakan yayin taron manema labarai, darektar shirye-shirye na kasa da kasa kan makon Michelle Meyrick, ta bayyana cewa, makon cinikayyar zai baiwa kananan 'yan kasuwa damar ganawa da masu masana'antu na kasar Sin tare da cin gajiyar abubuwan da za a kawo yayin makon.

Ta kara da cewa, makon zai baiwa 'yan kasuwar kasar Moccoro damar ganin kamfanonin kasar Sin da idanunsu, bullo da wata dama ta musamman ta tattaunawa tare da kulla dangantakar cinikayya da kasuwanci.

Shawarar nan ta Ziri daya da hanya,ita ce ta kai ga bijiro da wannan mako, wanda a halin yanzu ya samu nasara a kasashe da dama.

Kimanin kamfanoni 100 ne daga kasashen Morocco da Sin ake saran za su halarci makon, baya ga baki kimanin 4,000 daga sassan daban-daban.

Bayanai na nuna cewa, ya zuwa yanzu an gudanar da makon a kasashen hadaddiyar daular Larabawa, Kenya, Afirka ta kudu, Ghana da kuma kasar Habasha.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China