in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani game da rikicin siyasar kasar Zimbabwe
2017-11-20 13:25:24 cri

Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe ya yi shekaru 37 yana rike da ragamar mulki a kasarsa. A karshen shekarar bara, jam'iyya mai mulkin kasar ZANU-PF ta ba shugaba Mugabe damar sake wakiltarta wajen yin takarar neman samun kujerar shugaban kasa a babban zaben da zai gudana a shekarar 2018. Hakan ya sa shugaban ya yi alkawarin aiki har zuwa lokacin da shekarunsa za su kai 99. Sai dai rikicin siyasa da yanzu ake fuskanta a kasar ya haifar da wani yanayi na rashin tabbas ga niyyar da shugaban ya dauka.

An haife Robert Gabriel Mugabe a shekarar 1924, wanda ya taka muhimmiyar rawa a kokarin 'yantar da kasarsa daga mulkin mallaka. Kafin ya zama dan siyasa, ya taba karatu a kasar Afirka ta Kudu, inda ya yi karatu a Jami'a daya da Nelson Mandela.

A shekarar 1960, Robert Mugabe ya koma kasarsa da ake kira "Southern Rhodesia" a lokacin, inda ya kafa jam'iyyar ZANU, tare da jagorantar ayyukan yaki da mulkin mallaka. A shekarar 1963 ne hukumar Southern Rhodesia ta kama shi, tare da jefa shi gidan kurkuku. Ya yi zaman shekaru 11 a gidan yari kafin a sake shi. Daga bisani ne kuma ya tafi kasar Mozambique, inda ya ci gaba da gudanar da ayyukan neman 'yancin kan kasarsa.

Bisa kokarin da shi Robert Mugabe da abokan aikinsa suka yi, kasar Zimbabwe ta samu 'yancin kai a shekarar 1980, inda ya zama firaministan kasar na farko. Zuwa shekarar 1987 ne aka canza tsarin siyasar kasar, inda shugaban kasar ya samu cikakken ikon mulki maimakon firaministan. Kuma tun daga wancan lokacin ne Robert Mugabe ke zaman shugaban kasar, har zuwa yanzu.

A shekarun 1980, ana yi kasar Zimbabwe lakabi da 'Kwandon burodi na nahiyar Afirka', ganin yadda take fitar da abinci iri-iri ga kasashen waje. Sai dai tsarin mulkin mallaka ya sa yawancin gonakin kasar sun koma karkashin mallakar Turawa fararen fata, yayin da yawancin al'ummar kasar bakar fata, suka mallaki gonaki kadan. Don sauya wannan yanayi na rashin daidaito, sai gwamnatin Mugabe ta gabatar da manufar saye filayen gonaki daga hannun fararen fata, sa'an nan ta rabawa bakaken fata marasa gonaki. Inda gwamnatocin Zimbabwe da Birtaniya ke biyan kudin da ake bukata.

A sa'i daya Mugabe ya bukaci a samu masalaha tsakanin al'ummomin kasar. Kiran da ya sa ya samu yabo sosai.

Sai dai zuwa karshen shekarun 1990, kasar Birtaniya ta daina samar da kudi ga aikin "saye da raba gonaki". Al'amarin da ya kara lalata tattalin arzikin kasar, ya kuma sa aka kasa samun isashen kudin gudanar da aikin "saye da raba gonaki". Hakan ne ya sa Mugabe da jam'iyyarsa ta ZANU-PF suka gabatar da wata sabuwar manufa a shekarar 2000, inda aka fara kwace gonaki daga hannun fararen fata, ake rabawa ga bakaken fata masu bukatu. Manufar da ta sanya al'ummar kasar bakaken fata fiye da dubu 300 samun gonaki.

Sai dai sabuwar manufar ta fusata fararen fata masu gonaki, lamarin da ya haifar da zanga-zanga, da rikicin da ya kai ga zub da jini a kasar, har ya kai ga fararen fata da dama sun janye jarin da suka zuba a kasar Zimbabwe. Ban da haka kuma, sai kasashen yammacin duniya suka sanyawa kasar takunkumi, lamarin da ya sabbaba lalacewar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani a kasar.

Ban da matsalar tattalin arziki, sauran batutuwa masu alaka da siyasa su ma sun taimaka wajen haifar da rikicin siyasa a kasar a wannan karo.

Ita uwargidan shugaba Mugabe, Grace Marufu, 'yar siyasa ce dake da tasiri cikin harkokin siyasar kasar. A shekarar 2014, an zabe ta a matsayin babbar sakatariyar kwamitin siyasa na jam'iyyar ZANU-PF mai rike da ragamar mulkin kasar. Daga bisani kuma, sai ta fara matsawa Joice Mujuru, mataimakiyar shugaban kasa a lokacin lamba. Duk da cewa ita Mujuru tsohuwar 'yar siyasa ce da ta taba halartar yakin neman 'yancin kan kasar Zimbabwe, wadda kuma ake kallo a matsayin mai jiran gadon mukamin shugaba Mugabe, an tsige ta daga mukaminta a watan Disamban 2014.

Daga bisani shugaba Mugabe ya nada hannun damansa Emmerson Mnangagwa a matsayin mataimakin shugaban kasa. Sai dai zuwa wannan shekara da muke ciki, Madam Grace Marufu ta zargi Mnangagwa da kwadayin mulki a wurare daban daban, inda zuwa watan Nuwamba da muke ciki, aka tube shi daga matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, lamarin da ya sanya shi yin gudun hijira zuwa ketare.

Daga bisani dai, sojojin kasar sun dauki makatai, inda suka yi wa shugaba Mugabe da iyalinsa daurin talala. Daga nan, kasar Zimbabwe ta tsunduma cikin yanayin ricikin siyasar da ake fuskantar yanzu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China