in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta gabatar da shawarwari kan yadda za a warware batun Myanmar
2017-11-20 11:31:07 cri

Kasar Sin ta yi imanin cewa, kasashen Myanmar da Bangladesh za su iya warware batun jihar Rakhine ta hanyar tattaunawa.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da babbar jami'ar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi, ya ce, akwai bukatar kasashen duniya da kwamitin sulhu na MDD su gindaya wasu shadurra da samar da yanayin da ya dace na gudanar da wannan tattaunawa. Mr. Wang ya ce kasar Sin a nata bangare ta gabatar da wasu shawarwari guda uku game da yadda za a warware batun jihar Rhakine ta kasar ta Myanmar.

Na farko, ya kamata a hada gwiwa don cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta yadda mazauna yankin za su zauna a mahallansu.

Na biyu ya kamata kasashen duniya su karfafawa kasashen Myanmar da Bangledesh gwiwar ci gaba da tattaunawa ta yadda za a samu hanyoyin warware wannan batu cikin ruwan sanyi. Ya ce, yanzu haka kasashen biyu sun cimma yarjejeniya kwashe 'yan gudun hijira dake barin Myanmar zuwa kasar Bangladesh.

Na uku, shi ne a samu hanyoyin kawo karshen wannan matsala baki daya. Yana mai jaddada cewa, talauci shi ne musabbabin duk wani tashin hankali. A don haka, jami'in na kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa matakan da ake dauka na kawar da talauci a jihar Rhakine.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China