in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin kasar Kenya: yadda Sin ta zamanantar da tsarin kare muhallin halittu shi ne gishikin samar da daidaituwar al'amurra a duniya
2017-11-20 10:52:01 cri
Wani kwararran masani dan kasar Kenya ya bayyana cewa, tsarin da kasar Sin ke amfani da shi a halin yanzu na zamanantar da shirinta na kare muhallin halittu zai kawo daidaituwar al'amurra a duniya baki daya, wanda hakan ya shafi bangarori da dama da suka hada da batun sauyin yanayi, tashe tashen hankula, koma bayan tattalin arziki, da kuma batun ta'addanci.

Kagwanja ya ce, sabon tsarin da kasar Sin ta bullo da shi mai taken zamanantar da tsarin kula da muhalli yana samun karbuwa cikin sauri, inda ya kai wani sabon mataki da zai iya shawo kan matsalolin rashin tabbas wajen magance rikicin kan iyakokin kasashen duniya, ya bayyana hakan ne a cikin wani dogon sharhi da aka wallafa a jaridar Sunday Nation daily ta kasar. A 'yan shekarun nan, kasar Sin ta daga martabar shirinta na kiyaye muhallin halittu inda ta zamanantar da shi domin ya zama wani abin koyi a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da cigaban muhalli.

Kagwanja ya lura cewa, tsarin na kasar Sin zai iya tallafawa tsarin kare muhallin halittu na duniya ta yadda za'a iya yin amfani da muhallin wajen kyautata zaman rayuwar alumma da samar da cigaban tattalin arziki.

Ya kara da cewa, zamanantar da tsarin kiyaye muhallin halittu na kasar Sin ya samu karbuwa a duniya, ya ce dole a yabawa kokarin kasar ta Sin game kyautata mu'amalarta, da samar da cigaba, da kuma shirinta na samar da cigaba ta hanyar rage sinadaren dake gurbata muhalli. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China