in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samar wa Congo-Brazzaville taimakon jin kai na gaggawa
2017-11-19 13:38:27 cri
A ranar 17 ga wata, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Congo-Brazzaville ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin ta samarwa kasar Congo-Brazzaville kudaden taimakon jin kai kimanin dalar Amurka miliyan 6, domin taimaka mata wajen sassauta tabarbarewar yanayin jin kai a lardin Pool, sakamakon tashe-tashen hankulan da aka yi a wannan lardi.

A yayin taron manema labarai da aka yi a wannan rana, ministar kula da harkokin jin kai da zamantakewar al'umma na kasar Antoinette Dinga Djondo, ta yi godiya matuka ga gwamnatin kasar Sin, ta kuma kara da cewa, tun lokacin da kasarta ta fara neman taimakon jin kai daga gamayyar kasa da kasa, ya zuwa yanzu, gaba daya ta samu kudin taimakon jin kai na dalar Amurka miliyan 12, cikin har da kudin taimakon jin kai na dalar Amurka miliyan 6 da kasar Sin ta ba ta. Kuma, ta yi imani cewa, kasar za ta samu isassun kudaden taimakon jin kai kamar yadda take bukata.

Wakilin kungiyar samar da abinci ta kasa da kasa wato WFP da wakilin hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijirar MDD wato UNHCR sun halarci taron, inda suka kuma nuna yabo ga kasar Sin dangane da babban taimako da ta baiwa kasar Congo-Brazzaville.

Bugu da kari, wakilin kungiyar WFP ya bayyana cewa, yawan kudin taimakon jin kai da gwamnatin kasar Sin ta samarwa kasar Congo-Brazzaville ya kasance taimakon kudi mafi yawa, tun lokacin da kasar Congo-Brazzaville ta fara neman taimakon kudi, hakika kudaden za su taimaka matuka ga kasar wajen warware matsalar dake gabanta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China