in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron Intanet na duniya karo na hudu
2017-11-17 13:05:17 cri



Kasar Sin za ta karbi bakuncin taron Intanet na duniya karo na 4, wanda zai gudana daga 3 zuwa 5 ga watan Disambar bana a garin Wuzhen na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin.

Taron zai mai da hankali kan raya tattalin arziki bisa fasahohin sadarwar zamani, da kara bude kofa ga juna, domin raya harkokin Intanet cikin hadin-gwiwa. A halin yanzu, an shirya tsaf domin gudanar da wannan taro.

Daga shekara ta 1994 ne kasar Sin ta fara amfani da kafar sadarwa ta Intanet. Kawo yanzu, Sin ta zama babbar kasa a duniya wadda ke amfani da yanar gizo ta Intanet. A wajen taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya yi a jiya Alhamis, mataimakin darektan hukumar kula da harkokin Intanet ta kasar Sin Ren Xianliang ya ce, tattalin arzikin dake da alaka da Intanet a kasar Sin na bunkasa cikin sauri, inda ya ce:

"A 'yan shekarun nan, tattalin arziki mai alaka da yanar gizo ta Intanet na bunkasa cikin saurin gaske a kasar Sin, al'amarin da ya taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasar baki daya. A bara, adadin yawan tattalin arziki mai alaka da Intanet ya kai kudin Sin Yuan tiriliyan 22.4, wanda ya kai kashi 30.1 bisa dari na adadin yawan GDP na kasar Sin. Kana, yawan kudin cinikayya da aka yi ta kafar Intanet ya kai Yuan tiriliyan 26, kuma yawan kayan da ake saye da sayarwa ta Intanet ya karu da kashi 30 bisa dari a kowace shekara. Har wa yau, yawan mutanen da suke amfani da yanar gizo ta Intanet ya kai miliyan 750 a kasar Sin."

A wajen babban taron Intanet na duniya a wannan karo, za'a gudanar da dandalin tattaunawa, da bikin baje-koli kan harkokin Intanet, da taron nuna ci gaban harkokin Intanet na duniya, kana, za'a kira sauran wasu tarurrukan tattaunawa guda 20, wadanda suka shafi tattalin arziki mai alaka da Intanet, da fasahohin zamani, da dangantakar dake tsakanin Intanet da zaman rayuwar al'umma, da sa ido kan harkokin Intanet da sauran makamantansu.

Game da hakan, Ren Xianliang ya yi bayani cewa:

"Na farko, taron zai maida hankali kan ayyukan kirkire-kirkire, wanda zai tattauna kan makomar Intanet a nan gaba, da sauran wasu batutuwan da suka shafi amfani da na'ura mai kwaikwayar tunanin bil'adama. Na biyu, taron zai tattauna kan yadda dan Adam zai iya samun alfanu daga Intanet, da dangantakar dake tsakanin Intanet da zaman rayuwar al'umma, da sauran wasu batutuwan da suka jibanci rawar da kafar sadarwar Intanet ke takawa a fannonin tallafawa matalauta, da yaki da bala'u, da kiyaye al'adu. Dukkan wadannan batutuwa sun shaida cewa, Sin babbar kasa ce dake daukar nauyi bisa wuyanta."

Ita kuma a nata bangaren, mataimakiyar darektan kwamitin shirya babban taro a wannan karo, Madam Ge Huijun ta ce, bikin baje-kolin sabbin fasahohin zamani na Intanet na duniya shi ma ya kasance wani muhimmin abu a yayin taron. Madam Ge ta ce:

"Wasu shahararrun kamfanonin sadarwar Intanet na Sin da na duniya za su nuna sabbin nasarori, da fasahohinsu na zamani, ciki har da Alibaba, da Baidu, da Huawei, da kamfanin SAP na Jamus da sauransu. A yayin taron kuma, za'a yi baje-kolin sauran wasu na'urorin dake amfani da fasahohin zamani, inda jama'a za su iya samun damar gwadawa."

A halin da ake ciki yanzu, an riga an shirya tsaf domin gudanar da babban taron Intanet a wannan karo. Bisa hasashen da aka yi, akwai baki 1500 daga gida da waje wadanda za su halarci taron. Baya ga wasu sanannun kamfanonin Intanet na kasar Sin, shugabannin wasu mashahuran kamfanonin Intanet na duniya za su halarci taron, ciki har da Microsoft, Cisco, Oracle, Qualcomm, Intel, da kuma IBM. A nasa bangaren, mataimakin darektan hukumar kula da harkokin Intanet ta kasar Sin Ren Xianliang ya ce, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta wajen fadada bude kofa ga kasashen ketare, kana, tana maraba da kamfanonin sadarwar Intanet na kasashe daban-daban su zo nan Sin, domin more ci gaban harkokin Intanet. Mista Ren ya ce:

"Har kullum kofar kasar Sin a bude take ga duk duniya baki daya, ciki har da harkokin sadarwar zamani ta Intanet. Kasar Sin tana maraba da dukkanin kamfanonin Intanet na kasashe daban-daban, da yi musu maraba da zuwa nan kasar domin raya harkokinsu, da more nasarori gami da ci gaban fasahohin Intanet tare da kasar ta Sin." (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China