in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da takwaransa na kasar Australia
2017-11-15 13:24:13 cri
Jiya da safe ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da takwaransa na kasar Australia Malcolm Turnbull a birnin Manila, fadar mulkin kasar Philippines.

A yayin ganawar tasu, Li Keqiang ya bayyana cewa, ya kamata a kiyaye tsarin ciniki cikin 'yanci domin tabbatar da adalci. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Australia domin kiyaye yanayin ciniki cikin 'yanci, da kara bude kofa a fannin ciniki da zuba jari, ta yadda za a tabbatar da yin ciniki cikin adalci, da tabbatar da ganin an samu dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya.

A nasa bangare, Mr. Turnbull ya ce, dangantakar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasar Australia tana bunkasa cikin yanayi mai kyau, kana za a ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban a nan gaba. Haka kuma, kasashen biyu suna goyon bayan yin ciniki cikin 'yanci, a don haka, ya kamata a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Australia a wannan fanni, domin inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.

Sa'an nan kuma, ya ce, kasar Australia ta yabawa kasar Sin bisa kokarin da take yi na neman bunkasuwar yankin cikin lumana, tana kuma son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da Sin a fannonin kasuwanci, yin ciniki ta intanet, martaba dokoki da dai sauransu, ta yadda za a raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China