in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru a Afrika sun tattauna game da dokokin da suka shafi jirage marasa matuka
2017-11-15 09:39:42 cri
Kwararru a fannin sufurin jiragen sama na Afrika sun gana a Kigali babban birnin kasar Rwanda inda suka cimma matsaya game da amfani da dokokin da suka shafi amfani da jirage marasa matuka.

Masanan sun halarci wani taron karawa juna sani ne na kwanaki 3 wanda aka shirya game da batun tsarin amfani da kananan jiragen yaki wanda hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa da kasa ICAO da hadin gwiwar ofishin hukumar na gabashi da kudancin Afrika ESAF suka shirya.

Taron ya samu halartar kwararru daga hukumomi da fannonin sufurin jiragen sama 60 daga kasashen gabashi da kudancin Afrika 14 da kuma jamhuriyar Nijer.

Mahalarta taron za su nazarci manyan kalubalolin da suka shafi batun jirage marasa matuka ne domin duba hanyoyin da za'a gujewa fuskantar haddura ta hanyar mutunta dokokin da suka shafi fannin sufurin jiragen sama, da masu gudanar da harkokin sadarwa na tashi da saukar jiragen saman.

Da yake jawabi a lokacin taron, ministan sufurin kasar Rwanda Jean de Dieu Uwihanganye, ya bayyana bukatar dake akwai wajen aiwatar da dokokin da suka shafi harkar sufurin jiragen sama.

Ya ce jirage marasa matuka suna amfani da manyan fasahohin zamani, kuma a halin yanzu ana amfani da su har ma daga wasu bangarorin da ba na soja ba.

Ya ce dole ne a dinga mutunta dokokin kuma a aiwatar da su bisa la'akari da yadda ake samun yawaitar amfani da kananan jiragen sama. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China