Kamfanin mai hedkwata a birnin Wuhan na kasar Sin, ya bayyana a cikin wani sako da ya wallafa a adireshinsa na Wechat cewa, aikin samar da wutar lantarki na Mambila, shi ne aiki mafi girma da kamfanin yake gudanarwa a tarayyar Najeriya kana aikin samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa mafi girma da kamfanonin kasar Sin suka taba gudanarwa a ketare.(Ibrahim)