in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fidda littafi mai ba da shawara kan jinyar ciwon sukari da likitancin gargajiya na Sin
2017-11-14 11:06:24 cri

Yau Talata ne aka gudanar da taron manema labarai, don gabatar da littafi mai ba da shawara game da jinyar ciwon sukari, da likitancin gargajiya na kasar Sin a birnin Shenzhen dake nan kasar Sin.

Wannan shi ne littafi na farko da kungiyar ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin ta kasashen duniya ta fidda, domin ba da shawara kan jinyar wani ciwon musamman a fannin likitancin gargajiya na kasar Sin.

A yayin taron, mataimakin shugaban ofishin kula da manufofi da aikin sa ido na hukumar likitancin gargajiyar kasa ta Sin Yang Rongchen ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana bukatar tsara wasu ka'idojin da za a yi amfani da su tsakanin kasa da kasa, wajen yin musayar ra'ayoyi kan harkokin likitancin gargajiyar Sin, da gudanar da taruka masu nasaba da hakan, da ba da horaswa, da yin nazari kan ilmin likitancin gargajiyar Sin da dai sauransu.

Kaza lika ya dace kasar Sin ta ba da jagoranci kan wannan aiki, domin ita ce asali a wannan fanni na likitanci.

A nasa bangare kuma, babban sakataren kungiyar ilmin likitancin gargajiyar kasa ta Sin ta kasashen duniya ya bayyana cewa, an gabatar da wannan littafi ne domin ana sa ran neman wata sabuwar dabara, ta tsara littattafan ba da shawara kan jinyar cututtuka, da harkokin likitancin gargajiyar kasar ta Sin. Haka kuma, ana fatan za a iya fitar da littafin zuwa sauran kasashen duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China