Dr Francis Mangeni, masanin harkokin ciniki kuma daraktan kasuwanci na kasuwannin gabashi da kudancin Afrika yace, kamata ya yi kasashen su yi taka tsan-tsan game da kafa yankin ciniki maras shinge na nahiyar wato (CFTA) a takaice.
Ya bayyana cewa, yarjejeniyar kafa tsarin na CFTA zai cika ne a watan Disamba.
A wata sanarwa da masanin ya fitar yace, akwai matukar hadari dake tattare da aiwatar da shirin cikin gaggawa, yace an tsara shirin na CFTA ne ta yadda ba'a yi la'akari da wasu batutuwa ba musamman wadanda suka shafi batun tsawwala kudaden haraji a manyan hajojin wanda hakan zai iya zama koma baya ga harkokin cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar ta Afrika. (Ahmad)