in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Congo(Brazzaville): Ana mai da hankali kan horas da malamai 'yan kasar wajen koyar da Sinanci
2017-11-14 10:30:58 cri

Jami'ar Marien Ngouabi, jami'a ce daya tak mallakar gwamnatin kasar Congo(Brazzaville), inda a watan Maris na shekarar 2013, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Denis Sassou-Nguesso, suka halarci bikin kaddamar da laburare, da dakin nune-nunen kasar Sin a jami'ar, wadanda wani kamfanin kasar Sin ya taimaka wajen ginawa.

Ana tafiyar da kwalejin Confucius ne a dakin nune-nunen kasar Sin dake jami'ar. Yanzu sakamakon kyautatuwar mu'amala a tsakanin kasashen 2 a sassa daban daban, ya sa yawan matasa 'yan kasar Congo(Brazzaville) masu sha'awar koyon Sinanci suna ta karuwa.

A wasu makarantun sakandare, an kaddamar da kos din koyar da Sinanci, amma malamai suna bukatar kyautata kwarewarsu. A kokarin horas da karin malamai 'yan kasar Congo(Brazzaville), wadanda suka gwanance wajen koyar da Sinanci, kwalejin Confucius ta jami'ar Marien Ngouabi na kara taka muhimmiyar rawa.

Madam Li Na, shugabar kwalejin Confucius a jami'ar Marien Ngouabi ta yi mana bayani da cewa, a kokarin taimakawa makarantun sakandare na wurin wajen koyar da Sinanci, kwalejin Confucius ta ba da taimako wajen tsara kundin koyarwa, horas da malamai, sa ido kan koyar da Sinanci, tsara takardun jarrabawa da kuma dudduba takarun jarrabawa. Musamman ma a fannin horas da malamai, kwalejin ta ba da babban taimako wajen koyar da Sinanci a wurin yadda ya kamata. Li Na ta ce, "Mun samu sakamako mai kyau wajen horas da malamai masu koyar da Sinanci. A bara, mun gudanar da kos din farko na horas da malamai 'yan kasar Congo(Brazzaville) masu koyar da Sinanci 15. Dukkansu sun gama karatunsu ne daga kwalejinmu. Yanzu suna koyar da Sinanci a makarantun sakandare. Sakamakon samun isasshun malamai, ya sa tun daga watan Oktoban bara, aka fara koyar da Sinanci a dukkan makarantun sakandare guda 15 a Brazzaville."

Passy Ntoumba ya taba koyon Sinanci a jami'ar ilmin harsuna ta Beijing a shekaru 1980. Yanzu shi ne jami'i na farko mai sa ido kan aikin koyar da Sinanci a ma'aikatar kula da ilmin farko ta Congo(Brazzaville). Yana ganin cewa, taimakon da kwalejin Confucius a jami'ar Marien Ngouabi take bayarwa wajen horas da malamai 'yan kasar Congo(Brazzaville) masu koyar da Sinanci yana da muhimmanci matuka, kuma ya zama abun wajabi ne sosai."Mun samu taimakon kwalejin Confucius. A baya ba mu da isassun littattafai ta fuskar koyon Sinanci a makarantun sakandarenmu. Amma yanzu matasanmu suna iya karanta littattafan da suke sha'awa a nan kwalejin Confucius. 'Yan makarantun sakandarenmu sun kyautata kwarewarsu ta yin magana da Sinanci sakamakon karatu a nan."

OVA Sote, wani saurayi ne mai shekaru 26 a duniya. Yana karatu yana kuma aiki a kwalejin Confucius ta jami'ar Marien Ngouabi, dalibi ne kuma direba a kwalejin. Yana iya mu'amala cikin Sinanci ba tare da wata matsala ba. A watan Satumban bana, a matsayinsa na daya daga cikin malamai da dalibai 21, wadanda suke karatu a kwalejin Confucius a jami'ar Marien Ngouabi, ya samu damar zuwa kasar Sin, inda ya yi karatu da yin mu'amala a jami'ar Jinan. Saurayin ya gaya mana cewa, "A bana, yayin da muka ziyarci kasar Sin, ni ne jagoran dalibai. Mun ziyarci wurare masu ni'ima da yawa. Mun kara fahimtarmu kan halin da kasar Sin take ciki a halin yanzu. Muna da namu ra'ayi kan ko kasar Sin tana da kyau, ko a'a. Mun kara saninmu kan tarihin kasar Sin, da al'adunta. Yanzu mun san wurare da dama a kasar Sin. Dukkanmu mun yi matukar farin ciki!"

Madam Li Na ta yi bayani kan yadda kwalejin Confucius dinsu ke horas da malamai 'yan kasar Congo(Brazzaville) masu koyar da Sinanci. "Kwalejinmu ta hada kai da ofishin jagorantar aikin yayata Sinanci a duniya na kasar Sin, wajen horas da malamai 'yan kasar Congo(Brazzaville) masu koyar da Sinanci. Sa'an nan kwalejinmu ta hada kai da ma'aikatar kula da ilmin farko ta Congo(Brazzaville), wajen sake horas da wadannan malamai. Dabararmu ta yi amfani. Muna fatan za mu ci gaba da aikinmu, a kokarin kyautata kwarewar malamai a fannin Sinanci da koyar da Sinanci, ta yadda za a daga matsayin koyar da Sinanci a dukkan makarantun sakandare a nan Congo(Brazzaville)." (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China