in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen sojin saman kasar Sin August 1 sun nuna bajintarsu a atisayen jiragen sama na Dubai
2017-11-13 11:10:36 cri
Shida daga cikin jiragen sojojin saman yaki na kasar Sin wato August 1 samfurin J-10, sun nuna kwarewarsu a karon farko a tarihi a wani bikin nune nunen kwarewar jiragen sama da aka gudanar a Dubai karo na 15, wato Dubai Airshow.

Shen Jinke, kakakin rundunar sojojin 'yantar da al'umma ta kasar Sin PLA, ya bayyana tun a farkon wannan watan cewa, dakarun sojojin saman Sin sun riga sun shirya domin yin musaya da kuma kara yin hadin gwiwa da wasu bangarori a matakai daban daban da rundunonin sojojin sama na kasashen duniya domin bayar da gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasashen duniya.

Mahalarta daga kasashen duniya da dama sun bayyana farin cikinsu dangane da irin bajintar da dakarun sojin na kasar Sin suka nuna.

Omar Alhoshan, mai kamfanin jiragen sama na Alhoshan, wanda kamfaninsa ke kasar Saudiyya ya bayyana cewa, nune-nunen ya bayyana wasu muhimman bayanai. Ya kara da cewa sun kalli kyawawan dabarun sojin sama, ya ce lamari ne mai muhimmanci bisa yadda kasar Sin ta dauki yankin Gulf da muhimmanci. Kasar Sin babbar mai ta'ammali da harkokin sufurin jiragen sama ce, don haka dole ne su halarci bikin nuna kwarewa a fannin jiragen saman.

Bikin nune nunen na Dubai Airshowa na kwanaki 5 ne wanda za'a karkare a ranar Alhamis. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China