in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sayar da kayayyakin yuan biliyan 168.2 a 11 ga wata a Tmall
2017-11-13 11:08:45 cri

Daga karfe 12 na tsakar daren ranar 10 zuwa karfe 12 na tsakar daren ranar 11 ga wannan wata da muke ciki, kamfanin Alibaba ya sayar da kayayyakin da darajar su ta kai kudin Sin RMB ko yuan biliyan 168.2, a kasuwar yanar gizo ta Tmall, a ranar nan ta gaggarumin bikin sayen kayayyaki na bana. Masu sayayya a fadin duniya sun yi cinikin kayayyaki a duk tsawon ranar har sau biliyan 1 da miliyan 480.

A ranar 11 ga wata, kamfanin Alibaba wanda daya ne daga cikin manyan kamfanonin dake gudanar da kasuwanci ta yanar gizo a kasar Sin, ya sayar da kayayyaki da dama har na RMB ko yuan biliyan 168.2, adadin da ya kai matsayin koli a tarihin kamfanin. A ciki, adadin kasuwancin da aka biya kai tsaye ta yanar gizo ya kai kaso 90 bisa dari, kana saurin cinikin ya kai sau dubu 256 a ko wace dakika, kuma masu sayayya a kasashe da shiyyoyi 225 a fadin duniya sun shiga wannan gaggarumin bikin sayen kayayyaki.

Wannan rana, jagoran kamfanin Alibaba Zhang Yong ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka samu irin wannan babban sakamako a bana shi ne, kasancewar an hada kasuwancin kasuwa da kasuwanci ta yanar gizo yadda ya kamata, haka kuma kasuwanci ya samu ci gaba a nan kasar Sin, da ma sauran kasashen duniya baki daya, ya ce, "A ranar 11 ga watan Nuwambar bana, mun sake sa kaimi kan ci gaban kasuwancin kasar Sin, da kasuwancin kasashen duniya, a cikin kayayyakin da muka sayar a wannan rana, adadin kayayyakin da kamfanonin kasashen waje suka samar ya kai kaso 40 bisa dari, kuma cikin sauki masu sayayya na kasar Sin suna iya sayen kayayyaki masu inganci kai tsaye a nan kasar Sin ta yanar gizo, tare kuma da jin dadin hidima ta gari da ake samarwa. A sa'i daya kuma, muna yin kokarin sayar da kayayyakin da kamfanonin kasar Sin ke samarwa zuwa ga masu sayayya na kasashen waje, da kokarin dake samun karbuwa matuka daga wajen kamfanonin kasar Sin."

Yanzu haka bikin sayen kayayyaki na ranar 11 ga watan Nuwamba ya riga ya zama gaggarumin biki a fadin duniya, kuma abu mai faranta ran mutane a bikin na bana shi ne, masu sayayya sun fi nuna sha'awa kan kayayyakin da kamfanonin kasashen ketare suka samar. Misali yanzu adadin kamfanonin dake sayar da kayayyaki a kasuwar Tmall ya kai dubu 140, daga cikinsu kuma adadin kamfanonin ketare dake sayar da kayayyaki a kasuwar ya kai dubu 60. Kusan dukkan kamfanonin kasashen duniya suna sayar da kayayyaki a kasuwar Tmall, kuma aikinmu shi ne jigilar kayayyakin zuwa ga masu sayayya cikin lokaci.

Kwararre na CBN wato China Business Network Li Xuefeng ya yi nuni da cewa, "Cudanyar tattalin arzikin kasashen duniya ta kara habaka sannu a hankali, mu ma muna kara mai da hankali kan wannan. Misali a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2016 da ta gabata, adadin kamfanonin ketaren da suka sayar da kayayyaki ta yanar gizo a Tmall kaso 25 bisa dari ne, amma a shekarar 2014, adadin ya kai kaso 18 bisa dari, don haka a bayyane take cewa adadin na karu a kai a kai."

Jon Bright, 'dan kasar Australia ne wanda ke gudanar da cinikin jar barasar innabi a duk fadin duniya, ya kumsamu babbar moriya daga wajen habakar cudanyar tattalin arzikin kasashen duniya, tun bayan da aka fara yin amfani da dandalin biya kudi na Alipay. Jon Bright ya samu riba mai tsokaci daga kasuwanci ta yanar gizo, kuma kwanakin baya ba da dadewa ba, ya sake zuwa nan kasar Sin domin jin dadin gaggarumin bikin sayen kayyayaki na ranar 11 ga watan Nuwamba, tare kuma da neman samun sabbin damammakin ciniki, ya ce, "Ingancin jar barasar innabin da kamfaninmu ke samarwa, ya kai matsayin koli a kasarmu ta Australia, wurin da kamfaninmu yake ma ya zama wurin nishadin da ya fi samun karbuwa sosai daga wajen masu yawon bude ido a kasarmu. Ba ya ga su kan su masu yawon shakatawa na Australia da suke zuwa kamfaninmu ziyara, akwai kuma wasu da dama na kasashen ketare su ma suna zuwa yawon shakatawa; musamman ma masu yawon shakatawa da suka fito daga kasar Sin da dama da suke zuwa, adadin da ya karu da matukar mataki. A saboda haka, kamata ya yi mu samar musu hanyar biyan kudi mafi dacewa. A karkashin irin wannan hali, dandalin Alipay ya warware matsalarmu. A sanadin haka, muna gudanar da hadin gwiwa tsakaninmu yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China