Babban jami'in hukumar ya ce an dauko 73,943 daga cikinsu ne daga Kenya, yayin da aka kwaso 33,921 daga Yemen. Sauran sun hada da 589 da aka dauko daga Djibouti da 34 daga Eretria sai 2 daga Tunisia da kuma 1 daga Pakistan.
An kiyasin cewa, al'ummar Somalia miliyan biyu ne suka rasa matsugunansu, biyo bayan rikicin da ya haifar da daya daga cikin matsalolin jin kai mafi muni a duniya da ta kusa cika shekaru 30 a kasar.
Masana na ganin cewa, ci gaba da samun daidaituwar siyasa da tsaro a Somalia, tare da matsin lamba daga kasashen dake karbar 'yan gudun hijirar kasar, ya sa an mayar da hankali sosai kan samar da dawwamammiyar mafita ga 'yan gudun hijirar kasar. (Fa'iza Mustapha)