in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An daddale yarjejeniyoyin cinikin dala biliyan 250 tsakanin Sin da Amurka
2017-11-10 12:53:43 cri

Jiya Alhamis ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump suka halarci bikin rufe taron 'yan kasuwa na Sin da Amurka, inda suka kalli sanya hannu kan wasu kwangilolin ciniki da yarjejeniyoyin zuba jari a fannonin samar da makamashi da aikin kera kayayyaki da aikin gona da sauransu.

Ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta fayyace cewa, yayin ziyarar da shugaban Amurka Trump ya kawo a kasar Sin, gaba daya adadin yarjejeniyoyin hadin gwiwar da aka daddale tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 250, adadin da ya kai matsayin koli a tarihin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin Sin da Amurka, har ma ya kai matsayin koli a tarihin hadin gwiwar dake tsakanin daukacin kasashen duniya, game da wannan, shugaban kasar Sin Xi Jinping yana ganin cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin Sin da Amurka yana da babban karfi a asirce, haka kuma duk kan sassan za su amfana yadda ya kamata.

A matsayinsu na manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ya fi jawo hankalin al'ummun kasashen duniya. Jiya da safe ne a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, shugabannin kasashen biyu suka daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa 15 a fannonin samar da makamashi da aikin kirkire-kirkire da aikin gona da batun sararin samaniya dake tsakanin sassan biyu. Kana yayin ziyarar da shugaba Trump ya kawo a kasar Sin, gaba daya adadin yarjejeniyoyin hadin gwiwar da aka daddale tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 250, kuma a shekarar da ta gabata, adadin cinikin kayayyakin tsakanin sassan biyu ya kai dala biliyan 500, adadin da ya karu da ninki sama da 200 idan aka kwatanta da adadin shekarar 1979.

Yayin bikin rufer taron 'yan kasuwan Sin da Amurka da aka shirya jiya, shugaba Xi ya bayyana cewa, abubuwa a zahiri sun shaida cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin sassan biyu yana da babban karfi a asirce, haka kuma sassan biyu za su iya samun moriya tare, ya ce, "Kasar Sin kasa ce mafi girma mai tasowa a duniya, yayin da Amurka kuwa kasa ce mafi girma mai ci gaba, ya kamata kasashen biyu su gudanar da hadin gwiwa, a maimakon yin takara, muna fatan sassan biyu za su kara habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin shigo da kayayyakin gona dana makamashi daga Amurka, tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwa a fannin aikin samar da hidima, kana muna fatan Amurka za ta kara fitar da kayayayakin yau da kullum na zamani da al'ummun ke amfani da su zuwa kasar Sin, ko shakka babu za mu kara sa kaimi kan kamfanonin kasar Sin domin su kara zuba jari a kasar ta Amurka, muna fatan kamfanoni da hukumomin kudi na Amurka za su shigo cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya', ta yadda za mu kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninmu."

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, haka kuma za ta ci gaba da samar da wani muhalli mai inganci ga kamfanonin kasashen waje dake nan kasar Sin, ya ce, "Bude kofa ga kasashen waje babbar manufa ce ta kasar Sin wadda za a canja ba, kasar Sin za ta kara kyautata tsarin bude kofa bisa manyan tsare-tsaren da aka tsara yayin babban taron wakilan JKS karo na 19, ta yadda za a samar da wani muhalli mai inganci ga kamfanonin kasashen waje, ciki har da kamfanonin kasar Amurka."

A sa'i daya kuma, shugaba Xi ya bayyana cewa, bisa karuwar hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Amurka, kila za su gamu da wahalhalu, shi ya sa dole su yi kokarin kara fahimtar juna bisa tushen daidai wa daida da moriyar juna, su daidaita sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari.

A nasa bangaren, shugaba Trump ya bayyana cewa, Amurka tana son kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki dake tsakaninta da kasar Sin, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwa a fannin samar da makamashi, ta yadda kasashen biyu za su kara samun wadata, ya ce, "Aminai mahalartan wannan taro, rawar da kuke takawa tana da muhimmanci matuka ga zaman lafiya da wadatan kasashen biyu, hadin gwiwar da muke gudanarwa tsakaninmu zai samar mana da makoma mai haske, muna fatan za ku yi koyi da juna, domin kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakaninmu, tare kuma da cimma ra'ayi guda a wannan fannin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China